Kano: Allah ya yi wa gogaggen dan siyasa kuma fitaccen dattijo, Dangalan, rasuwa

Kano: Allah ya yi wa gogaggen dan siyasa kuma fitaccen dattijo, Dangalan, rasuwa

- Allah ya yi wa Malam Muhammadu Dauda Dangalan na jihar Kano, rasuwa

- Marigayin na daga cikin jiga-jigan da suka kafa tsohuwar jam'iyyar NEPU da PRP

- An yi jana'izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a gidansa dake Fagge

Muhammadu Dauda Dangalan, dattijon da ya kasance daya daga cikin jiga-jigan da suka kafa tsohuwar jam'iyyar NEPU da PRP, ya riga mu gidan gaskiya a garin Kano.

Daruruwan masu ta'aziyya sun samu halartar jana'izarsa wacce aka yi a gidansa dake kwatas din Fagge a birnin Kano. Daga bisani an birne shi a makabartar Kofar Mazugal a yammacin ranar Asabar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kwatanta mutuwar fitaccen dan siyasan da faduwan babban ginshikin damokaradiyya.

Dangalan, wanda rayuwarsa ya sadaukar da ita a siyasa da gwagwarmaya, ya fara siyasarsa ne tuna zamanin jamhuriya ta farko.

KU KARANTA: Kotun daukaka kara ta wanke matar da ake zargi da sheke mijinta ta hanyar yi wa mijinta allurar guba

Kano: Allah ya yi wa gogaggen dan siyasa kuma fitaccen dattijo, Dangalan, rasuwa
Kano: Allah ya yi wa gogaggen dan siyasa kuma fitaccen dattijo, Dangalan, rasuwa. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

"A madadin gwamnati da jama'ar jihar Kano baki daya, ina mika ta'aziyyar mutuwar Malam Dauda Dangalan ga iyalansa, jama'ar jihar Kano da dukkan talakawan dake fadin Najeriya," Ganduje yace.

Kamar yadda Gwamnan ya sanar a ta'aziyyarsa, Alhaji Dangalan ya sha gwagwarmayar siyasa duk domin amfanin talakawa.

KU KARANTA: Kotun daukaka kara ta wanke matar da ake zargi da sheke mijinta ta hanyar yi wa mijinta allurar guba

A wani labari na daban, ragowar daliban kwalejin harkar noma da gandun dabbobi da ke Afaka a Mando, jihar Kaduna an kwashesu zuwa barikin Div 1 Garrison Command a Kaduna.

Legit.ng ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka shiga makarantar inda suka kwashe dalibai mata.

Wata majiya daga rundunar soji ta sanar da Daily Trust cewa ba don kokarin jami'an rundunar sojin sama ba da na Div 1 dake Kaduna, da harin sai ya fi haka kazanta.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit

Online view pixel