Za mu tabbatar ɗaliban da aka sace sun dawo gida lafiya, in ji Gwamnatin Kaduna

Za mu tabbatar ɗaliban da aka sace sun dawo gida lafiya, in ji Gwamnatin Kaduna

- Gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta tabbatar da ganin ta ceto daliban da aka sace

- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan

- Mr Aruwan ya kuma yaba wa kokarin jami'an tsaro saboda amsa kira cikin gaggawa da dakile sace wasu daliban

Gwamnatin jihar Kaduna, a ranar Lahadi ta ce abinda ta mayar da hankali a kai shine tabbatar da ceto dalibai 39 da aka sace daga Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Afaka, ƙaramar hukumar Igabi, rahoton Daily Trust.

Tunda farko rahotanni sun bayyana cewa daliban da suka hada da mata 23 da maza 16 suna hannun masu garkuwar inda suke neman a biya su N500m kafin su sako su.

Za mu tabbatar ɗaliban da aka sace sun dawo gida lafiya, Gwamnatin Kaduna
Za mu tabbatar ɗaliban da aka sace sun dawo gida lafiya, Gwamnatin Kaduna. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan wasu mutane masu raƙuma da suka ɓulla a Kano

Gwamnatin jihar ta bakin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, a ranar Lahadi ya ce sun jinjinawa ƙoƙarin jami'an tsaro wurin ceto daliban kwalejin 180.

Aruwan ya ce gwamnati jihar na tare da sojoji, DSS, yan sanda da sauran jami'an tsaro wadanda suka yi gaggawar kai ɗauki hakan yasa maharan ba su sace wasu daliban ba.

KU KARANTA: 'Yan bindiga kai hari sansanin ƴan sanda, sun kashe sufeta da farar hula

"A halin yanzu gwamnatin jihar Kaduna ta mayar da hankali kan abu guda ne kawai shine ganin daliban sun dawo lafiya sannan a cigaba da tattara bayanan sirri da sa ido don kiyaye afkuwar irin wannan a gaba," in ji shi.

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel