Buhari na samun bayanan duk abinda ke faruwa a yankin Arewa maso gabas, Inji CDS
- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na sane da duk abinda ke faruwa da jami'an tsaron da aka turo yankin Arewa maso gabas
- Shugaban Ma'aikatar tsaro, Janar Lucky Irabor yakai ziyara hedkwatar 'Operation lafiya dole' a jihar Borno
- CDS ya bayyana cewa suna bayyana ma shugaban duk abubuwan dake wakana a yankin kuma shima yana bibiyar lamarin
Shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yana da cikakken bayani akan dukkanin lamuran da suka shafi ayyukan dakarun dake Borno da sauran yankin arewa maso gabas.
Irabor, ya kara da cewa shugaban yana bin dukkanin abubuwan dake faruwa a hedikwatar Operation Lafiya Dole da sauran sassan Ƙasar nan.
KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: 'Yan sanda sun harbe wasu masu garkuwa da mutane a Abuja
Ya fadi hakan ne a jiya yayin wata ziyara da yakai jihar Borno, inda ya yaba ma dakarun Operation Lafiya Dole kan jajircewar su da sadaukarwa a watan da ya gabata
Ya lura da cewa dakarun sun samu nasarori da dama da ya cancanci a yaba musu sosai. Leadership ta ruwaito.
Yace Shugaban Kasa yana sane da duk wasu al'amura da suka shafi aikin, kuma tabbas idan muka koma zamu kara bashi cikakken bayani.
KARANTA ANAN: Wani Kansilan unguwa a jihar Kano ya kaddamar da hadimansa na mulki mutum 18
A bayaninsa shugaban tsaron yace:
"Abinda nake so ku sani shine shugaban kasa ya bamu umarni kuma wannan umarnin dole mu cika shi."
"Wannan yasa muke aiki ba kakkautawa domin ganin dukkanin wasu rikice-rikice da rashin tsaro musamman a cikin yankin Operation Lafiya Dole an kawo karshen su"
“Zamu cigaba da aiki sosai kuma muna fatan cikin kankanin lokaci duk wani waje dake wannan yanki na Operation Lafiya Dole ya dawo hannun hukumomin kasa" Shugaban ya bayyana
Wannan dai itace ziyarar aiki ta biyu da shugaban ma'aikatan tsaron da shugabannin tsaron suka kawo tun bayan nadin da akai musu.
Shugaban ma'aikatan tsaron yaje Maiduguri a 31 ga watan Janairu, sati guda bayan nadin shi tare da sauran shuwagabannin tsaro.
A wani labarin kuma Shehu Sani ya bayyana yadda 'yan bindiga suka kara zama abin tsoro a Kaduna
Ya yi magana ne dangane da yunkurin satan mutane da aka yi kokarin dakilewa a rukunin gidajen ma'aikatan tashar jirgin saman Kaduna da safiyar Lahadi.
Tsohon sanatan Ya bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta magance irin wadannan matsaloli a yankunan
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, Ya fara aiki kwanan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha ɗake garin wudil jihar Kano. Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77
Asali: Legit.ng