Dakarun sojin Najeriya sun yi wa 'yan bindiga ruwan wuta a Chikun

Dakarun sojin Najeriya sun yi wa 'yan bindiga ruwan wuta a Chikun

- Zakakuran sojin rundunar Operation Thunder Strike sun yi nasarar halaka 'yan bindiga biyu a Chikun

- Sojojin da dakarun sun yi musayar wuta ne a kan babbar hanyar Gwagwada zuwa Chikun dake karamar hukumar Chikun

- An samu nasarar daukar gawawwakin 'yan bindiga biyu, bindiga daya, sunkin wiwi da wasu wayoyin salula biyu

Dakarun rundunar Operation Thunder Strike sun halaka 'yan bindiga biyu a wani smamen da suka kai cikin dare wurin babban titin Gwagwada zuwa Chikun dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, wannan na kunshe ne a wata takarda da Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna ya fitar a ranar Asabar.

Yace kamar yadda dakarun suka sanar, rundunar ta yi amfani da damar da ta samu wurin bibiyar kaiwa da kawowar 'yan bindigan.

'Yan bindigan sun tunkaro a babura biyu, lamarin da yasa dakarun suka bude musu wuta kuma suma suka yi martani.

KU KARANTA: Da duminsa: Ragowar daliban makarantar da 'yan bindiga suka kai farmaki sun koma barikin sojoji

Dakarun sojin Najeriya sun yi wa 'yan bindiga ruwan wuta a Chikun
Dakarun sojin Najeriya sun yi wa 'yan bindiga ruwan wuta a Chikun. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

A take kuwa dakarun suka sheke 'yan bindiga biyu yayin da sauran suka tsere da miyagun raunika.

Bayan musayar wutan, an samu gawawwakin 'yan bindigan biyu tare da wayoyi biyu, babur daya, bindigar toka daya da wasu sunkun wiwi.

Gwamna Nasir El-Rufai ya jinjinawa dakarun tare da mika musu godiya. Ya kara da taya su murnar nasarar wannan lamarin yayin da yake jinjinawa kwazonsu.

KU KARANTA: Mun tsiyace, ba mu da kudi yanzu – Majalisar Wakilan Tarayya ta fito, ta koka

A wani labari na daban, shugaban majalisar sarakunan kasar nan kuma sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, a ranar Alahmis yace mulkin janar Aguiyi Ironsi, Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo ne suka bar masarautun gargajiya babu kundun tsarin mulkinsu.

A yayin jawabi a wani taro a Abuja ga kwamitin sake duban tsarin mulkin kasar nan na majalisar, ya ce dokar Ironsi ta 1966, Gowon ta 1967 da Obasanjo 1976 ne suka kwace karfin ikon sarakunan gargajiya suka mika ga kananan hukumomi.

Sarkin Musulmin wanda ya samu wakilcin Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, ya ce wadannan dokokin ne suka samar da rashin tsaro tare da rashawar da kasar nan ke fuskanta.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel