Mun tsiyace, ba mu da kudi yanzu – Majalisar Wakilan Tarayya ta fito, ta koka

Mun tsiyace, ba mu da kudi yanzu – Majalisar Wakilan Tarayya ta fito, ta koka

- Majalisar wakilan Najeriya ta koka da fatara tare da talaucin da take ciki kuma tana bukatar karin kaso

- Kamar yadda mai magana da yawun majalisar ya sanar, hakan ne yasa basu iya sauke nauyin mazabunsu

- A halin yanzu 'yan majalisar na karbar N800,000 da N8.5 miliyan duk wata amma akwai bukatar karin kaso

Majalisar wakilan tarayyar kasar nan tace ta talauce kuma kasafin da aka fitar mata ba dole ya amfani 'yan Najeriya ba.

Benjamin Kalu, mai magana da yawun majalisar ya sanar da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, cewa 'yan majalisar na cikin tsananin "fatara yayin da suke kokarin sauke nauyin mazabunsu dake kansu."

Kamar yadda The Cable ta ruwaito, 'yan majalisar tarayyar sun saba kokawa a kan albashin da ake biyansu na N800,000 da kuma N8.5 miliyan duk wata.

KU KARANTA: Kasaitattun fadar sarakuna 6 a Najeriya da kyawawan hotunansu

Mun tsiyace, ba mu da kudi yanzu – Majalisar Wakilan Tarayya ta fito, ta koka
Mun tsiyace, ba mu da kudi yanzu – Majalisar Wakilan Tarayya ta fito, ta koka. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

An kara kasafin majalisar tarayyar daga N125 biliyan a 2020 zuwa N128 biliyan a wannan shekarar.

Har ila yau, Kalu yace rashin darajar naira na daya daga cikin abinda ke tabarbara musu kasafi a kowacce shekara

"Majalisar ta talauce. Na fada a baya kuma ina sake fadin haka. Bana tsoron fadin hakan," yace.

"A yau dala ta kai har N400, yawan abinda kasafin zai iya siya ba daya yake da shekaru 10 da suka gabata ba."

Ya kara da cewa ya fuskanci shugabannin majalisar tarayyan inda ya tambayesu, "Me yasa kuke tsoron kara kasafin majalisa wanda kun san hakan ne zai bamu damar sauke hakkokin dake kanmu yadda ya dace?"

KU KARANTA: Namijin da ba zai iya ba budurwa N300K na kasuwanci ba, bai cancanci a aure shi ba, Uche

A wani labari na daban, sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Bamalli da sarkin Birnin-Gwari, Alhaji Zubairu Maigwari II, sun ce mutanensu sun biya daruruwan miliyoyi a matsayin kudin fansa ga 'yan bindiga.

Sun sanar da hakan ne yayin gabatar da rahoton tsaro na 2020 ga Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, The Nation ta wallafa.

Maigwari ya ce: "Abun takaici ne da tashin hankali ka ga 'yan bindiga 200 zuwa 300 dauke da makamai sun zagaye kauye suna kashe jama'a tare da karbe kudadensu. Jama'armu sun biya daruruwan miliyoyin naira a matsayin kudin fansa."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel