Da dumi: Kotun koli ta rage adadin zaman Kurkukun Joshua Dariye da shekaru 2, yanzu zai yi 10

Da dumi: Kotun koli ta rage adadin zaman Kurkukun Joshua Dariye da shekaru 2, yanzu zai yi 10

- A yau kotun koli ta kammala shari'ar tsohon gwamnan jihar Plateau Joshua Dariye

- Shekaru uku kenan Sanata Josha Dariye yana daura a gidan gyaran halin Kuje

- An yanke masa hukunci a shekarar 2018 kan laifin almundahana da babakeren dukiyar al'ummarsa

TVC ta rahoto cewa kotun kolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin zaman Kurkuku kan laifin yaudarar al'umma kan tsohon gwamnan jihar Plateau, Joshua Dariye.

Wannan ya biyo bayan rage adadin shekarun daga 14 zuwa 10 da kotun daukaka kara tayi kwanakin baya.

Za ku tuna cewa a shekarar 2018, babban kotun birnin tarayya karkashin jagorancin Alkali Adebukola Banjoko ta yankewa tsohon gwamnan hukuncin shekaru 14 a gidan maza.

Kotun koli a ranar Juma'a, 12 ga Maris, 2021 karkashin jagorancin Alkali Helen Ogunwumiju ta tabbatar da cewa lallai tsohon gwamnan ya yaudari al'ummarsa kuma zai kwashe shekaru 10 a gidan gyaran hali.

Amma kotu ta yi watsi da tuhumar almundahanan da aka yi masa wanda ke dauke da tarar shekaru 2 a gidan yari.

Yanzu bisa wannan shari'a ta karshe, Sanata Joshua Dariye zai cigaba da zama a gidan yari har sai bayan shekaru 10.

DUBA NAN: Alhaji Dantata zai dauki nauyin karatun dalibai 100 a sabuwar jami'ar Al-Istiqama

Da dumi: Kotun koli ta rage adadin zaman Kurkukun Joshua Dariye da shekaru 2, yanzu zai yi 10
Da dumi: Kotun koli ta rage adadin zaman Kurkukun Joshua Dariye da shekaru 2, yanzu zai yi 10
Source: Twitter

DUBA NAN: Muna sake jaddadawa, ba za'a kara farashin litan man fetur ba a watan nan, NNPC

Tsakanin 2015 da ya hau mulki zuwa yanzu, wasu tsaffin gwamnoni kuma mambobin jam'iyyar APC sun shiga gidan yari.

Daga cikinsu akwai Jolly Nyame, Orji Uzor Kalu, James Bala Ngilari dss.

Lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ofis a shekarar 2015, ya bayyana cewa zai yi yaki da cin hanci da rashawa.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel