Wike ya zargi Buhari da siyasantar da tallafin biliyan 10 da aka bai wa jahar Lagas

Wike ya zargi Buhari da siyasantar da tallafin biliyan 10 da aka bai wa jahar Lagas

Gwamnan jahar Rivers, Nyesom Wike ya zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da siyasantar da tallafin naira biliyan 10 da ya amince a jihar Legas don yaki da cutar coronavirus.

Akalla mutane 234 ne suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya, inda jahar Lagas ke da mafi yawan wadanda suka kamu yayinda, jahar Rivers ke da mutum daya.

Gwamna Wike ya soki kokarin gwamnatin Buhari na yaki da cutar coronavirus da take yi, yana mai cewa Buhari ya maida abin siyasa, da hakan ke neman ya jefa Najeriya cikin halin kakanikayi idan ba a mai da hankali ba.

Ya ce, Jahar Legas ce cibiyar Kasuwancin Najeriya, amma kuma Rivers ita ce arzikin man kasar nan ke kwance jihar ta fi kowacce jiha samar wa Najeriya da kudaden shiga, saboda haka dole ita ma a bata wani kason kudin coronavirus, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Wike ya zargi Buhari da siyasantar da tallafin biliyan 10 da aka bai wa jahar Lagas

Wike ya zargi Buhari da siyasantar da tallafin biliyan 10 da aka bai wa jahar Lagas
Source: UGC

“Ban ga dalilin da zai sa gwamnatin tarayya ta tsame jiha daya tal ba. Ko tana nufin sai an samu akalla mutane 50 ne sun kamu da cutar za a ba jiha tallafi daga gwamnatin tarayya. Dukkan mu jihohin kasa daya ne, saboda haka kada a nuna fifiko akan wata jaha” cewar shi.

A karshe ya bayyana cewa mara lafiya daya da a ka samu ya na dauke da cutar coronavirus a jahar ya soma samun sauki., sannan kumacewa za a ba mutane dama su fita su garzaya kasuwa domin siyan kayan abincin bukin Easter a ranar Talata da Laraba.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Har yanzu ba a tabbatar da sakamakon gwaji na biyu da aka yiwa Gwamna Mohammed ba – Mataimakin gwamna

A gefe daya mun ji cewa an sake samun sabbin mutane biyu da suka kamu da cutar Covid-19 wacce aka fi sani da coronavirus a jahar Ogun. A yanzu jumlar mutane shida kenan suka kamu a jahar.

Gwamna Dapo Abiodun, wanda ya bayyana hakan a gidansa da ke Iperu, jahar Ogun yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu, ya ce wadanda suka kamun basu da wani tarihi na zuwa kasashen da annobar coronavirus ya barke kuma ba su hadu da mutanen da suka yi tafiya ba.

Abiodun ya ce wannan sabon lamari a jahar ya nuna cewa cutar baya la’akari da matsayi, shekara, jinsi ko kuma asalin mutum.

Ya ce yayinda daya ya zo daga Mowe a karamar hukumar Obafemi Owode da ke jahar, dayan ya fito ne daga karamar hukumar Yewa ta Kudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel