Masu kira ga gwamnati ta kama ni kidahumai ne, Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani

Masu kira ga gwamnati ta kama ni kidahumai ne, Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani

- Sheikh Ahmad Gumi ya mayar da martani da masu cewa ya kamata a kama shi

- Wannan shine karo na biyu da Malamain ya soki wasu kan zaman da yake yi da yan bindiga

- Sheikh Gumi ya shahara da ziyartar yan bindiga cikin daji domin yi musu wa'azi su ajiye makamai

Shahrarran Malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya caccaki dukkan masu kira ga gwamnati ta kamashi saboda ganawar da yake yi da yan bindiga.

Gumi ya siffanta masu hakan a matsayin kidahumai saboda ya kamata su san cewa tare da jami'an gwamnati suke zuwa ganawar da yan bindigan.

Yayin magana da Daily Post, Malamin ya bayyana cewa ba shi bane mutumin farko da zai tattauna da yan bindiga.

Yace, "Ko gwamnan jihar Kaduna ya zauna da su, gwamnan Zamfara ya zauna da su."

"Ba ni bane mutumin farko da zai tattauna da su ba. Ni kawai na kara nawa ne, kuma na gansu a matsayin mutane masu son addini; addini kadai ke koyar da cewa jini na da daraja."

"Ina kokarin tattara su ne in koyar da su darajar rayuwa. Ban taba ziyartar yan bindiga ba tare da wani jami'in gwamnati ba."

"Dukkan yan bindigan da muka gana da su tare da jami'an gwamnati ne, shi yasa nike kiran masu cewa a kamani kidahumai."

KU KARANTA: Gwamnatin Bayelsa ta kafa dokar hana makiyaya kiwo a faɗin jihar

Masu kira ga gwamnati ta kama ni kidahumai ne, Sheik Ahmad Gumi ya yi martani
Masu kira ga gwamnati ta kama ni kidahumai ne, Sheik Ahmad Gumi ya yi martani Credit: Sheikh Ahmad Gumi/Facebook
Asali: Facebook

DUBA NAN: Gwamnan Neja ya bada umurnin rufe dukkan makarantun sakandaren gwamnatin jihar

Gumi ya kara da cewa sulhu da yan bindigan na haifar da 'da mai ido.

"Tattaunawa da su ya kawo sakamako cikin sauri. Idan kana tattaunawa da mutumin da yayi zurfi cikin aikata laifi, idan ka je masa matsayin dan sanda, za ka samu matsala amma idan kaje masa matsayin Fasto, zai fada maka laifukan da yake aikatawa," Yace.

"Saboda haka muna zuwa musu a matsayin malamai, sai su samu kwanciyar hankali su bayyana mana matsalolinsu. Mu kuma sai muka yadda zamu kwantar musu da hankali."

"Ka san ko wani mutum na da addinin da yayi imani da shi, dalilin da yasa muke haka kenan," Ya kara.

A bangare guda, mai bada shawara kan lamarin tsaro, Babagana Monguno, ya bayyana cewa Sheikh Ahmadu Abubakar Gumi, ya yi musu alkawarin taimakawa gwamnati wajen magance matsalar tsaro.

A hira da manema labarai ranar Alhamis, Monguno, ya ce lallai ya gaba da Gumi, kuma yana sauraron yadda Malamain zai taimakawa gwamnati.

Sheikh Gumi ya kasance yana shiga dazuka domin ganawa da yan bindigan yana musu wa'azin ajiye makamai da neman tuba.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel