Abin da ya sa na maka Gwamnan jihar Taraba a kotu inji ‘Dan Majalisar Tarayya

Abin da ya sa na maka Gwamnan jihar Taraba a kotu inji ‘Dan Majalisar Tarayya

- Hon. David Fuah ya kai karar Gwamnan jihar Taraba, Mr. Darius Ishaku a kotu

- ‘Dan Majalisar ya na zargin Gwamnan da taso shi a gaba a binciken da ya ke yi

- Ana binciken Makarantar Taraba Poly, inda 'Dan Majalisar ya yi aiki kafin 2019

‘Dan majalisar jihar Taraba, Hon. David Fuah, ya kai karar gwamna Darius Ishaku zuwa kotu, ya kuma fadi abin da ya sa ya dauki wannan mataki.

Jaridar Punch ta yi hira da Honarabul David Fuah inda ya bayyana mata cewa ya shigar da karar gwamnansa ne domin ya hana shi taso shi a gaba.

‘Dan majalisar mai wakiltar mazabar Sardauna, Gashaka da Kurmi ya zargi gwamnatin Darius Ishaku da kokarin ganin bayansa a tafiyar siyasa.

David Fuah wanda ya rike shugaban kula da kudi na babbar makarantar koyon aiki ta jihar Taraba tsakanin 2016-19, ya ce Ishaku ya matsa masa.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun aukawa Nasarawa, sun kashe Mai gari da wasu mutane

A cewar ‘dan majalisar tarayyar, kwamitin da aka kafa ya binciki makarantar da ya yi aiki, ya na kokarin kakaba masa laifi ne da karfin tsiya da yaji.

Hon. David Fuah ya ke cewa:

“Ganin yadda aka kafa kwamitoci baro-baro da nufin su kama ni da laifi, sai na sheka kotu domin in hana wadannan kwamitoci zama su gudanar da aikinsu.”

“Amma saboda gwamnan ya na kokarin bata mani suna ta kowace irin hanya, ya ba kwamitocin damar cigaba da zama duk da an aiko masu takardar kotu.”

Abin da ya sa na maka Gwamnan jihar Taraba a kotu inji ‘Dan Majalisar Tarayya
Gwamna Darius Ishaku
Asali: UGC

KU KARANTA: EFCC na kokarin aika wadanda su ka saci kudi zuwa kurkuku - Bawa

“A dalilin haka ne na shirya tawagar lauyoyi su kai karar gwamnan da zargin yi wa kotu wasa da hankali, ya karbi aikin kwamitin da kotu ta kalubalanta.”

“Manufar kwamitocin binciken ita ce su bata mani suna, shiyasa sunana ya bayyana a rahoton na su duk da cewa umarni kurum na ke karba a makarantar.”

Dazu an ji cewa Gwamnatin Kaduna ta jaddada matakin ta na rashin yin sulhu da 'yan bindiga.

Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce 'yan bindiga sun kalubalanci karfin mulkin Najeriya don haka ya zama dole a shafesu daga duk inda su ke fake.

El-Rufai yayi wannan tsokacin ne a ranar Laraba yayin gabatar da rahoton tsaro na 2020 na jihar Kaduna. Jaridar The Cable ta ce ta fitar da wannan rahoton.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel