‘Yan Majalisa sun yi wa Gwamna Fayemi mubaya’a ya nemi kujerar Buhari a zaben 2023

‘Yan Majalisa sun yi wa Gwamna Fayemi mubaya’a ya nemi kujerar Buhari a zaben 2023

- Wata kungiya ta kai ziyara Majalisar dokokin Ekiti ta na tallata takarar Fayemi

- ‘Yan Majalisar Ekiti su na goyon bayan Kayode Fayemi ya nemi Shugaban kasa

- Duka ‘Yan Majalisar jihar sun ce za su goyi bayan Gwamna Fayemi ya yi takara

Majalisar dokokin jihar Ekiti, ta yi wa gwamna Kayode Fayemi mubaya’ar tsaya wa takarar kujerar shugaban kasa a zaben Najeriya mai zuwa na 2023.

Jaridar Daiy Trust ta rahoto cewa majalisar jihar Ekiti ta na goyon bayan shugaban kungiyar gwamnoni, Kayode Fayemi ya yi takarar shugaban kasa.

‘Yan majalisar na jihar Ekiti sun yi wa gwamnan mubaya’a ne a lokacin da ‘ya ‘yan wata kungiya da ake kira ‘Our Belief Project’, su ka ziyarce su a jiya.

Shugaban wannan kungiya ta ‘Our Belief Project’, Adewunmi Abejide, ya ce sun kai ziyara majalisar ne domin a matsa wa Fayemi ya nemi mulkin kasar.

KU KARANTA: Matasa da Mata su ka zugo ni in nemi Shugaban kasa – Yahaya Bello

Shugabar majalisar dokokin Ekiti, Funminiyi Afuye, ta karbi maganar Cif Adewunmi Abejide.

A madadin sauran ‘yan majalisar jihar Ekiti 26, Funminiyi Afuye, ta sha alwashin ganin an taso Kayode Fayemi a gaba har ya nemi takarar shugaban kasa.

Afuye, take cewa Fayemi ba zai bada kunya ba: “Ba ku bukatar ku kira mu, mu na tare da ku a batun nan, mun yi alkawarin ba ku cikakken goyon baya.”

Adewunmi Abejide, wanda ma’aikacin gwamnatin Ekiti ne, ya ce lokaci ya yi da ‘dan jihar zai mulki kasar nan, idan Muhammadu Buhari ya gama wa’adinsa.

KU KARANTA: Mutane 5 da ka iya maye gurbin Shugaba Buhari a zaben 2023

‘Yan Majalisa sun yi wa Dr. Fayemi mubaya’a ya nemi kujerar Shugaba Buhari a zaben 2023
Gwamnan Ekiti, Dr. John Kayode Fayemi
Source: Twitter

Shugabar majalisar ta ce Fayemi ya rike jihar Ekiti kamar yadda Obafemi Awolowa ya yi mulkinsa.

Cif Abejide ya ce sun samu goyon bayan sarakuna da manyan kasar Yarbawa wadanda su ke ganin cewa Fayemi ne ya dace ya rike Najeriya a shekarar 2023.

Ku na sane cewa har yau Fayemi bai fito fili ya nuna sha’awar neman mulkin Najeriya ba, amma magoya-baya su na cigaba da ba shi kwarin gwiwar jarraba sa’arsa.

Fayemi wanda yake wa’adin karshe a matsayin gwamna, shi ne shugaban kungiyar NGF. Kafin yanzu ya taba rike Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit

Online view pixel