Bidiyo: Sunday Igboho ya aike da jan kunne da kakkausar murya ga 'yan sanda, soja da DSS

Bidiyo: Sunday Igboho ya aike da jan kunne da kakkausar murya ga 'yan sanda, soja da DSS

- Sunday Igboho, mai rajin kare hakkin Yarabawa ya ja kunnen sojoji, 'yan sanda da jami'an DSS

- Yayi kira garesu da kada su ga 'yan uwansa Yarabawa da bindiga su kashesu kamar yadda Buhari ya bada umarni

- A cewarsa, suna amfani da bindigoginsu ne domin baiwa kansu kariya idan zasu shiga gonakinsu

Fitaccen mai rajin kare hakkin Yarabawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya ja kunnen jami'an tsaro a kan bibiyar mafarauta ko masu gadi dake amfani da bindigogi.

Ya sanar da hakan ne a wani bidiyo da tsohon minsitan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya wallafa a Twitter.

Ya ce, "Muna farin ciki da umarnin halaka duk makiyayin da aka kama da AK-47 da shugaban kasa ya bada. Duniya za ta san abinda makiyaya ke yi da kuma wanda suka yi. Muna farin ciki da umarnin shugaban kasa.

KU KARANTA: Jihar Kano za ta karba kasonta na riga-kafin korona a ranar Talata

Bidiyo: Sunday Igboho ya aike da jan kunne da kakkausar murya ga 'yan sanda, soja da DSS
Bidiyo: Sunday Igboho ya aike da jan kunne da kakkausar murya ga 'yan sanda, soja da DSS. Hoto daga @Thenation
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon gagarumin mai safarar miyagun kwayoyi, Bishi Taiwo, da NDLEA ta kama

"Mun ga amfanin duk abubuwan da muka dinga fadi. Makiyayan nan na amfani Ak-47 ne domin garkuwa da mutane, fashi, fyade da kuma neman fitina, amma mun godewa Ubangiji da maganganunmu suka yi amfani.

"Abinda nake so cewa shine, 'yan sanda, jami'an hukumar tsaro ta farin kaya da sojoji, gwamnati ta bada umarnin harbesu a take idan an kama su da Ak-47 suna barna, muna so ku san cewa Sheikh Gumi ya nuna muku inda makiyayan nan suke.

"Bai ce ku nuna bangaranci ba. Bai ce ku je kasar Yarabawa ko ta Ibo ku fara kashe jama'a ba.

"Kada ku ga mutum da bindiga a cikin 'yan uwana Yarabawa saboda tsaro suke amfani da su ku kuma ku harbesu. Kada ku kuskura ku fara hakan.

"Kada daga kun ga mutum da bindiga ku manna masa sharri ku halaka shi.Muna rokon ku da ku kasance masu adalci."

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta ja kunnen fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Gumi, da ya guje zubdawa rundunar mutunci.

Daraktan hulda da jama'a na rundunar, Birgediya janar Mohammed Yerima a wata takarda da ya fitar ya ja kunne malamin da ya kiyaye yadda zai dinga kwatanta rundunar sojin.

Ya ce: "Hankalin rundunar sojin Najeriya ta kai kan wani bidiyo da ke nuna fitaccen malami Sheikh Ahmed Gumi yana zargin sojojin da ba musulmi ba da harar 'yan bindiga."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel