El-Rufai: Ba zan taɓa sulhu da ƴan bindiga ba, bana goyon bayan yi wa ɓata-gari afuwa

El-Rufai: Ba zan taɓa sulhu da ƴan bindiga ba, bana goyon bayan yi wa ɓata-gari afuwa

- Nasiru El-Rufai gwamnan jihar Kaduna ya sake nanata cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da yan bindiga ba

- Har way yau, gwamnan na Kaduna ya ce baya goyon bayan yi wa yan bindiga ko wasu bata gari afuwa

- Gwamna El-Rufai ya yi wannan furucin ne a wurin bada rahoton tsaro na shekarar 2020 a gidan gwamnatin jihar Kaduna

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya sake jaddada cewa ba zai taba yin sulhu da yan bindiga ba kuma baya goyon bayan yi wa bata gari da ke adabar jiharsa afuwa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin gabatar da jawabinsa na rahoton tsaro ta shekarar 2020 da aka yi a gidan gwamnati a Kaduna.

El-Rufai: Ba zan taɓa sulhu da ƴan bindiga ba, bana goyon bayan yi wa ɓata-gari afuwa
El-Rufai: Ba zan taɓa sulhu da ƴan bindiga ba, bana goyon bayan yi wa ɓata-gari afuwa. Hoto: @KadunaGov
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Matawalle ya bawa ƴan bindiga wa'addin watanni biyu su tuba su miƙa makamansu

Mr El-Rufai ya nanata cewa abinda ya dace shine ragargazar yan bindiga, barayin shanu da yan daba har sai sun rasa yadda za su yi sun "mika wuya ga hukuma sun bi doka."

A cewarsa, bai kamata a bata lokaci ba wurin kawar da bata garin.

Ya ce, "Matsayar mu a Kaduna a fili ta ke karara, dole a yaki yan bindiga, barayin shanu da yan daba har sai sun bi doka.

"Ba za mu yi sulhu da masu laifi ba kuma ba mu goyon bayan duk wani yunkuri na yi musu afuwa.

KU KARANTA: Dama ta samu: An sake buɗe shafin bada tallafin rancen COVID-19 daga bankin CBN

"Kungiyoyin bata gari, yan bindiga, yan ta'adda da masu yaki da sunan kabila ko addini sun yanke shawarar cewa za su kallubalanci yancin Nigeria sannan su addabi jama'ar mu. Ya zama dole a kawar da masu laifin ba tare da bata lokaci ba."

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel