Hotunan masu zanga-zanga da suka mamaye majalisar dattawa

Hotunan masu zanga-zanga da suka mamaye majalisar dattawa

- Mambobin kungiyar ma'aikatan majalisun kasar nan sun fito zanga-zanga akan hana mahukunta 'yancinsu

- Fusatattun ma'aikatan sun mamaye majalisar tarayya dake Abuja dauke da fastocin bukatunsu

- Sun yi barzanar mamaye dukkan majalisun jihohin kasar nan 36 nan da kwanaki 6 idan ba a biya musu bukatunsu ba

Mambobin kungiyar ma'aikatan majalisu ta Najeriya a ranar Talata sun yi zanga-zanga inda suka mamaye majalisar dattawa dake Abuja, Channels TV ta wallafa.

A yayin zanga-zangar, ma'aikatan sun yi barazanar cewa za su mamaye dukkan majalisun jihohin fadin kasar nan idan ba a biya musu bukatarsu ba.

Shugaban kungiyar, Mohammed Usman, wanda yayi jawabi a madadin 'yan kungiyar inda yace 'yan majalisar tarayya sun dauka matakin da ya dace wurin baiwa ma'ikatar shari'a 'yancinsu saboda walwalar mambobinsu na tattare da wannan 'yancin.

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon gagarumin mai safarar miyagun kwayoyi, Bishi Taiwo, da NDLEA ta kama

Hotunan masu zanga-zanga da suka mamaye majalisar dattawa
Hotunan masu zanga-zanga da suka mamaye majalisar dattawa. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

"Ya isa haka. Idan babu mahukunta, babu kasar baki daya. Suna so su hana 'yancin mahukunta mu kuwa ba zamu bari ba. Idan suka cigaba da hana 'yancin, za mu yi amfani da duk karfinmu wurin yakarsu.

"Nan da kwanaki shida idan ba a tabbatar ba, zamu mamaye dukkan majalisun jihohi 3 na fadin kasar nan har da majalisar tarayya," Usman ya sanar da manema labarai yayin zanga-zangar.

Hotunan masu zanga-zanga da suka mamaye majalisar dattawa
Hotunan masu zanga-zanga da suka mamaye majalisar dattawa. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamnatin Kwara ta sake garkame makarantu 10 a kan rikicin Hijab

A wani labari na daban, ma'aikatar ilimi ta jihar Kwara ta soke hukuncinta na sake bude wasu makarantu 10 na jihar inda aka yi rikicin saka hijab.

Kamar yadda babbar sakatariyar ma'aikatar, Kemi Adeosun ta tabbatar, da farko an bukaci makarantun su bude a ranar Litinin amma an soke hakan.

Ta ce wannan hukuncin an yanke shi ne saboda wasu dalilan tsaro, Premium Times ta wallafa. "A don haka gwamnatin take umartar 'yan makarantun da malamansu da su zauna a gida akasin sanarwar farko da aka yi."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng