Yanzun nan: 'Yan bindiga sun sake sace mutum 19 a wani kauyen jihar Neja

Yanzun nan: 'Yan bindiga sun sake sace mutum 19 a wani kauyen jihar Neja

An sace akalla mutane 19 a kauyen Kutunku da ke cikin karamar hukumar Wushishi ta jihar Neja a ranar Litinin, The Nation ta ruwaito.

Wadanda aka sace sun hada da maza goma sha daya da mata takwas ciki har da amare biyu da za su yi aure a karshen makon nan.

'Yan bindigar sun afkawa kauyen ne a kan babura suna harbi ba ji ba gani.

An ce sun buge wasu daga cikin mutanen garin wadanda ba su iya tserewa a kan lokaci ba.

Wata majiya a yankin ta shaida wa manema labarai ta wayar tarho cewa 'yan bindigar sun mamaye gidaje kuma sun kwashe makudan kudade da kayan abinci.

Majiyar ta ce 'yan bindigar ba su tuntubi al'ummar da iyalan mutanen da aka sace ba.

Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, DSP Wasiu Abiodun ya ci tura domin bai amsa kiran da aka masa ba.

Karin bayani na kusa...

Asali: Legit.ng

Online view pixel