56 Miliyan 'Yan APC Suka Ba 'Yan Ta'adda Don Su Riƙe Daliban Da Suka Sace a Jangeɓe, Dr. Shinkafi

56 Miliyan 'Yan APC Suka Ba 'Yan Ta'adda Don Su Riƙe Daliban Da Suka Sace a Jangeɓe, Dr. Shinkafi

- Shugaban jam'iyyar APGA ya zargi APC da ƙoƙarin rura wutar sace-sace a jihar Zamfara

- Ya Zargi jam'iyyar ta APC da saka siyasa wajen matsalar rashin tsaro da yaƙi ci yaƙi cinyewa a faɗin jihar

- Shugaban yace shuwagabannin APC sun bawa 'yan bindigar da suka sace ɗalibai a Jangeɓe 56 miliyan a kan kada su sake su

Shugaban jam'iyyar (APGA) na jihar Zamfara, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, ya zargi shuwagabannin jam'iyyar (APC) da bawa yan ta'adda kuɗi don su riƙe ɗaliban Jangeɓe.

Ya yi zargin (APC) ta bada kuɗin da suka kai 56 miliyan da nufin kar su saki 'yan matan da aka sace a makarantar sakandiren kwana ta Jangebe.

Dr. Shinkafi wanda ya kasance tsohon ɗan takarar gwamna ne a jihar Zamfara a zaɓen 2019 da ya gabata. Vanguard ta ruwaito

KARANTA ANAN: Ranar mata: Matan Najeriya 3 da su ka yi gwagwarmayar da ba za a taba mantawa da su ba

Ya bayyana cewa 'yan (APC) suna ƙoƙarin ganin sun daƙile duk wani yunkurin da gwamnan yake yi wajen ganin an samu zaman lafiya a jihar.

A cewar shugaban: "Ina ƙalubalantar dukkanin 'yan siyasa daga kan jam'iyya mai mulki zuwa ta 'yan hamayya, da su miƙa wayoyinsu ga jami'an tsaro don su gudanar da bincike."

56 Miliyan Ƴan APC Suka Ba Ƴan Ta'adda Don Su Riƙe Daliban Da Aka Sace a Jengeɓe - Shinkafi
56 Miliyan Ƴan APC Suka Ba Ƴan Ta'adda Don Su Riƙe Daliban Da Aka Sace a Jengeɓe - Shinkafi Hoto: @Zamfara_state
Asali: Twitter

"Ina da tabbacin cewa sakamakon da binciken zai bayar zai matuƙar girgiza kowa," inji Shinkafi

KARANTA ANAN: Babu abin da zai hana ‘Dan Arewa cigaba da mulki bayan Buhari inji babban Gwamnan APC, Bello

Sannan yadda jami'an tsaron ya kamata suyi binciken shine su binciko tun daga ranar 25 ga watan Febrairu da ya gabata har ya zuwa lokacin da aka saki daliban.

Shinkafi ya ƙara da cewa akwai wasu 'yan (APC) da suka ƙuduri aniyar ganin cewa sai sunsa matawalle ya gaza wajen gudanar da ayyuka a jihar Zamfara.

Inda ya ƙara da kira ga jami'an tsaro akan buƙatuwarsu kara dagewa wajen magance matsalar tsaro.

Sannan yayi kira ga matasa akan kada su bari wasu gurɓatattun ƴan siyasa suyi amfani dasu wajen rikitar da kasa.

Ya kuma buƙaci matasan da su maida hankali wajen yin abubuwan raya ƙasa.

A wani labarin kuma Jihar Katsina ta gurfanar da Dr Mahadi Shehu a gaban kotu da zargin batanci

Ana Zargin mutumin da aikata laifin watsa bayanan batanci game da gwamnatin jihar ta Katsina

Kwamishinan shari'a na jihar ya tabbatar da cewa, kalaman da yake watsawa na karya ne.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwanan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel