Ranar mata: Matan Najeriya 3 da su ka yi gwagwarmayar da ba za a taba mantawa da su ba

Ranar mata: Matan Najeriya 3 da su ka yi gwagwarmayar da ba za a taba mantawa da su ba

A ranar 8 ga watan Maris na kowace shekara ce ake yin bikin ranar manyan mata ta Duniya.

A wannan shekarar, legit.ng Hausa ta tattaro maku wasu shahararrun matan da su ka yi fadi-tashi a Najeriya, tare da gajeren tarihin rayuwarsu.

Ga wadannan mata nan kamar haka:

1. Ransome-Kuti Olufunmilayo

An haifi Misis Funmilayo Ransome-Kuti ne a shekarar 1900 a garin Abeokuta (jihar Ogun a yau), ta rasu a 1978 ta na mai shekara 78 a Duniya.

Funmilayo Ransome-Kuti ta na cikin matan da su ka fara halartar makarantar Abeokuta Grammar a 1914, daga nan ta tafi kasar Ingila ta kara ilmi.

Bayan dawowar ta gida, ta yi gwagwarmaya sosai wajen ganin mata sun yi karatu da shiga siyasa. Daga cikin 'ya 'yanta akwai Fela Kuti.

2. Magaret Ekpo

Tarihi ya tabbatar da an haifi Margaret Ekpo ne a 1914, Mahaifinta Eyo Aniemewue ya fito ne daga gidan sarautar Eyo Honestry da Okoroafor Obiasulo.

KU KARANTA: Shahararrun ‘Yan kwallon Najeriya 10 da su ka fi kudi

Ranar mata: Matan Najeriya 3 da su ka yi gwagwarmayar da ba za a taba mantawa da su ba
Kuti, Ekpo da Sawaba Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Ekpo ta bar Najeriya ta tafi birnin Dublin a kasar Ireland, ta yi karatun Difloma a ilmin kimiyya a 1946, daga nan ta kafa ma’aikata a garin Aba ta kasar Abia.

Madam Margaret Ekpo ta taimaka wajen ganin mata sun kutsa harkar siyasa a Kudancin Najeriya. A 2006 ta rasu a wani asibiti a Kalaba ta na shekara 92.

3. Gambo Sawaba

Wannan jeri ba zai cika ba sai an hada da Hajiya Gambo Sawaba wanda aka haifa a shekarar 1933. Gambo Sawaba tana cikin jajirtattun matan da aka yi a Arewa.

An yi wa Gambo Sawaba aure ne tun tana ‘yar shekara 13, dole daga baya auren ya mutu bayan ta karbi kiran siyasar Malam Aminu Kano na jam’iyyar NEPU.

Babu wata mace a Najeriya da aka daure a gidan yari kamar Gambo (ta shiga kurkuku sau 16). Wannan Baiwar Allah ta rasu a asibitin ABUTH, Zaria a 2001.

‘Yar wasar fim dinnan, Anita Joseph ta yi sanadiyyar jawo abin magana bayan ta fito da wani bidiyon Mai gidanta ya na yi mata wanka a cikin bayan-gida.

Mabiya Instagram sun ga mijin ‘yar wasan kwaikwayo ya na cuda mata jiki a ban daki.

Anita Joseph ta wallafa bidiyon mijinta ya na yi mata wanka, wannan bidiyo ya jawo an dura kan ‘yar wasar, wasu kuma suna ganin hakan ba wani laifi ba ne.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel