An yanka ta tashi: ‘Yan Sanda sun cafke ‘Yan OPC da su ka kama 'Shugaban 'Yan bindiga'

An yanka ta tashi: ‘Yan Sanda sun cafke ‘Yan OPC da su ka kama 'Shugaban 'Yan bindiga'

- ‘Yan Sanda sun damke ‘yan kungiyar OPC da su ka cafke Iskilu Wakilin Ayete

- Ana zargin wadannan mutane da yin kisan-kai a wajen kama wannan mutumi

- ‘Yan OPC sun ce Iskilu Wakilin Ayete ne shugaban ‘yan bindigan da ke Ibarapa

Rundunar ‘yan sandan Najeriya sun cafke ‘yan kungiyar Oodua People’s Congress (OPC) a kan kama Iskilu Wakilin Ayete da su ka yi a jihar Oyo.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa jami’an tsaron sun yi ram da wadanda su ka cafke wannan mutumi da ake zargin cewa ya na garkuwa da mutane.

Ana zargin Iskilu Wakiliin Ayete shi ne shugaban ‘yan bindigan da su ke ta’adi a Ibarapa, jihar Oyo.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta reshen jihar Oyo, ta tabbatar da cewa ta cafke mutane uku daga cikin ‘ya ‘yan kungiyar OPC da su ka kama Wakiliin Ayete.

KU KARANTA: An kama gagararren 'dan bindiga da ya addabi yankin Ibarapa

Jami’an ‘yan sandan sun ce an yi wa wadannan mutane tambayoyi a game da kisan rai da su ka yi a wajen yunkurin kama wannan mutumi da ake zargi da laifi.

Mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar Oyo, Olugbenga Fadeyi, ya ce Kwamishinan ‘yan sanda, ya bada umarnin a wuce da Iskilu Wakiliin Ayetezuwa asibiti.

Jawabin ya ce: “Jami’an ‘yan sanda su na sanar da jama’a cewa da kimanin karfe 9:00 na safe, an kama wasu mutane uku da daga baya aka gana cewa ‘yan OPC ne.”

“Sun shiga yankin Kajola, a Ibarapa na jihar (Oyo), da nufin kama wani Bafullatanin mutumi, Wakili, wanda ake zargi da hannu a ta’adin da ake yi wa Yarbawa.”

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun yi ram da wasu bata-gari rututu a casun ‘Yan luwadi

An yanka ta tashi: ‘Yan Sanda sun cafke ‘Yan OPC da su ka kama 'Shugaban 'Yan bindiga'
Wakiliin Ayete
Asali: UGC

‘Yan Sanda su ka ce da ‘yan OPC din su ka shiga gidan Wakili, sun banka wuta, hakan ya sa su ka kona wata Baiwar Allah wanda har yanzu ba a gane wacece ita ba.

Jawabin ya karkare da cewa: “A karshe duk wanda ya ke da wani abu da Iskilu Wakili ya kai kara a ofishin CID da ke Iyaganku, Ibadan, domin a gudanar da bincike.”

Tsohon Mataimakin gwamnan Kaduna, Bernabas Bala Bantex, ya na tare da Maigidansa, ya soki matsayar Sheikh Ahmad Abubakar Gumi na yi sun sulhu da 'yan bindiga.

Bala Bantex ya bayyana irin ta'adin da 'yan bindiga su ka yi, sannan ya ce masu cin moriyar rashin tsaro ba za su yi sha’awar samun zaman lafiya a Najeriya ba.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel