Kashin wasu samari ya bushe, ‘Yan Sanda sun damke su a wajen bikin ‘Yan luwadi

Kashin wasu samari ya bushe, ‘Yan Sanda sun damke su a wajen bikin ‘Yan luwadi

- Dakarun 'Yan Sanda sun kama wasu Bayin Allah a bikin ‘Yan luwadi a Anambra

- An shirya wannan biki ne a wani otel da ke cikin karamar hukumar Dunukofia

- Jami’an tsaron sun cafke wasu a wajen wannan bikin, sun wuce ofishinsu da su

Jami’an ‘yan sanda na reshen jihar Anambra sun kama wasu mutane da yawa da ake zargin ‘yan luwadi ne a yankin karamar hukumar Dunukofia.

Jaridar Punch ta rahoto cewa an damke wadannan mutane ne a ranar Lahadi, 7 ga watan Maris, 2021.

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun ‘yan sandan sun kai samame ne a wani otel da ke Dunukofia, inda wadannan ‘yan luwadi su ke shirya bikin.

Rundunar ‘yan sandan sun yi nasarar auka wa wadannan shu’umai ne bayan an kyankyasa masu cewa wasu ‘yan luwadin sun shirya yin ‘casu’ a otel.

KU KARANTA: Masu gigin hana ayi karatun Al-Qur’ani zai gamu da azabar Allah - Dahiru Bauchi

Wata majiya daga rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa an kama mutane da-dama, ‘mafi yawancinsu duk maza ne masu mabanbantan shekaru.”

Wani mazaunin wannan gari ya tabbatar da abin da jami’an tsaron su ka fada, ya ce: “’Yan luwadin su na biki ne a otel din lokacin da rikici ya barke.”

Ya ce: “Wannan ya yi sanadiyyar da aka gayyato ‘yan sanda daga ofishinsu na yankin Ukpo.”

“Mutanen sun yi yunkurin su tsere a lokacin da ‘yan sanda su ka dura, hakan ya jawo aka tarwatsa saman dakuna da wasu kayan cikin wanan otel din.”

Kashin wasu samari ya bushe, ‘Yan Sanda sun damke su a wajen bikin ‘Yan luwadi
Gwamnan Anambra Willie Obiano
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamnonin Arewa ta gabas sun zauna a garin Bauchi, sun yi taro

An zarce da mutanen da aka kama zuwa babban ofishin ‘yan sanda da ke Ukpo domin cigaba da bincike.

Amma da aka tuntubi ‘yan sanda sun nuna ba su san maganar ba. Kakakin dakarun, Haruna Mohammed ya ce bai da masaniya a kan wannan lamarin.

A karshen makon nan ne mu ka ji wasu 'yan bindiga sunyi awon gaba da wani hamshaƙin ɗan kasuwa a Abia. Har yanzu dai babu labarin wannan mutum.

'Yan bindigar sun samu damar sace mutumin ne a daidai lokacin da yake jiran wani daga cikin iyalan gidansa ya fito ya buɗe masa kofa a garin Ogbunike.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit

Online view pixel