PDP ta murƙushe APC a zaben ƙananan hukumomi da Kansiloli a jihar Delta

PDP ta murƙushe APC a zaben ƙananan hukumomi da Kansiloli a jihar Delta

- Jam'iyar PDP ta murkushe jam'iyar APC da dukkan zaɓukan da akayi na kananan hukumomi a jihar Delta.

- Baturen zaɓen jihar ya bayyana haka a babban birnin jihar lokacin da yake karanto sakamakon zaben ranar Lahadi

- A cewarsa, zaben ya kammala a dukkan ƙananan hukumomin jihar 25, kuma duk PDP tayi nasara a dukkan su.

Jam'iyar PDP mai mulkin jihar Delta ta murƙushe abokiyar hamayyarta wato APC a zaɓukan da aka gudanar na ƙananan hukumomi a faɗin jihar.

Baturen zaɓen jihar, Chief Mike Ogbodu, ya bayyana haka yayin da yake karanto sakamakon zaɓukan a babban birnin jihar, Asaba.

KARANTA ANAN: Rashin tsaro: Tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna ya yi magana, ba ya goyon bayan Dr. Gumi

Ogbodu Yace, jam'iyar PDP ta samu nasara a dukkan zaɓen ƙananan hukumomi 25 da kansiloli 500 na faɗin jihar.

"(PDP) ce ta samu nasara a Zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar 6 ga watan maris, 2021," inji Baturen zaɓen.

PDP ta murƙushe APC a zaben ƙananan hukumomi da Kansiloli a jihar Delta
PDP ta murƙushe APC a zaben ƙananan hukumomi da Kansiloli a jihar Delta Hoto: @OfficialPDPNigeria
Source: Twitter

"Kamar yadda sakamakon zaben da aka tattara ya nuna, jam'iyyar (PDP) ta cinye dukkan ƙananan hukumomi da kuma kansiloli," a cewar Ogbodu.

Ya ƙara da cewa babu wani tashin hankali ko hatsaniya da aka samu a lokacin zaɓen da bayan kammala zaɓen.

KARANTA ANAN: Anita Joseph: Tauraruwar Nollywood ta wallafa bidiyon Mijinta ya na yi mata wanka

Wani ɗan takarar kansila ƙarƙashin jam'iyyar (APC), Mr. Samson Uwandulu, da jama'arsa sun nuna basu yarda da sakamakon da hukumar zaɓe ta jihar ta sanar ba.

Lokacin da yake fira da manema labarai, Ɗan takarar ya yi ikirarin cewa shine ya ci zaɓen kansila a unguwar Isele-Azagba, karamar hukumar Oshimili ta arewa.

Ya bayyana cewa baturen zaɓen yankin su ya sanar da cewa (APC) ta sami ƙuri'u 408, (PDP) nada 317.

Amma a cewarsa, kafin a tabbatar masa da nasarar sa sai masu ruwa da tsaki suka tsaida komai aka shiga aka fita aka canza sakamakon zaɓen.

Kamar yadda Jaridar Vanguard wallafa a shafinta, tace duk wani yunƙuri na samun jin ta bakin humar zaɓen jihar yaci tura.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun sace wani hamshaƙin ɗan kasuwa a jihar Abia

Har yanzin waɗanda suka sace shi basu tuntuɓi kowa ba domin aji manufarsu nayin awon gaba dashi

'Yan bindigar sun samu damar sace mutumin ne a daidai lokacin da yake jiran wani daga cikin iyalan gidansu ya fito ya buɗe masa kofa.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwanan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

za'a ita samunsa a shafin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuh77

Source: Legit

Online view pixel