'Yan bindiga sun sace wani hamshaƙin ɗan kasuwa a jihar Abia

'Yan bindiga sun sace wani hamshaƙin ɗan kasuwa a jihar Abia

- Wasu 'yan bindiga huɗu sunyi awon gaba da wani hamshaƙin ɗan kasuwa a Jihar Abia.

- 'Yan bindigar sun samu damar sace mutumin ne a daidai lokacin da yake jiran wani daga cikin iyalan gidansu ya fito ya buɗe masa kofa.

- Har yanzin waɗanda suka sace shi basu tuntuɓi kows ba domin aji manufarsu nayin awon gaba dashi

Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sunyi awon gaba da wani hamshaƙin dan kasuwa a garin Aba, jihar Abia.

Mutumin da aka sace mai suna, Mr. Kenechukwu Okeke, ɗan asalin garin Ogbunike ne a yankin karamar hukumar Oyi, jihar Abia.

KARANTA ANAN: Da duminsa: Dakarun soji sun fatattaki 'yan Boko Haram daga Borno

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, 'yan bindigan sun biyo mutumin ne kuma suka sami damar yin gaba dashi a lokacin da yake jiran wani daga cikin iyalansa ya buɗe masa kofa.

'Yan bindiga sun sace wani hamshaƙin ɗan kasuwa a jihar Abia
'Yan bindiga sun sace wani hamshaƙin ɗan kasuwa a jihar Abia Hoto: @Daily_trust
Asali: Twitter

Kuma sun sami damar sace shi ne a ƙauyen Umuozuo, karamar hukumar Osisioma.

KARANTA ANAN: Yawan kabilu da addinai ke jawo kalubale wajen gina Najeriya, Osinbajo

Har yazuwa yanzin waɗannan sukai wannan aika-aikar basu tuntuɓi kowa ba bare asan manufarsu.

Wata majiya a yankin, ta faɗawa jaridar The Nation a asirce cewa, sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa na kara yawaita a yankin a kwana kwanan nan.

Sun yi kira ga hukumomin tsaro na jihar da su ƙara zage dantse don shawo kan lamarin taɓarɓarewar tsaro a yankin da ma jihar baki ɗaya.

An nemi jami'in yaɗa labarai na hukumar yan sandan jihar amma ba'a same shi ba bare aji ta bakinsa.

A wani labarin kuma Gwamnati ta yi watsi da jita-jitar cewa zata kashe 10 biliyan wajen rarraba rigakafin corona

Shugaban hukumar lafiya ta ƙasa Dr. Faisal Shu'aib yace haɗakar ƙungiyoyi masu zaman kansu ne suka ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya.

Ya tabbatar da cewa sun tanaji jirgi da kuma motar zirga- zirga da zasu yi aikin rarraba kayan zuwa jihohin kasar nan .

Ahmad Yusuf dan mtan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Online view pixel