Wike: Ni nayi addu'a kada a samu tsaro a Nigeria saboda abinda Buhari ya yi wa Rivers a 2016

Wike: Ni nayi addu'a kada a samu tsaro a Nigeria saboda abinda Buhari ya yi wa Rivers a 2016

- Gwamna Nyesome Wike na jihar Rivers ya ce shine ya yi addu'ar kada a samu zaman lafiya a Nigeria

- A jawabin da Wike ya yi wurin bude asibitin gidan gwamnati, ya ce ya nemi taimako daga wurin Shugaba Buhari amma aka hana shi

- Ya ce daga wannan lokacin ne ya koma gida ya fadawa jama'arsa su koma ga Allah su yi addu'ar rashin zaman lafiya ya wanzu a kasar tunda an ki taimakonsu

Gwamnan Rivers, Nyesome Wike ya ce ya yi addu'ar Najeriya ta fuskanci kallibalen tsarp bayan gwamnatin tarayya ta ki aike wa da jami'an tsaro jihar Rivers a lokacin da jihar ke fama da kallubalen tsaro a 2016, News Wire ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi wurin bude asibitin gidan gwamnati da ofisoshi a Port Harcourt, babban birnin jihar a ranar Alhamis.

Na yi addu'ar kada a samu zaman lafiya a Nigeria saboda abinda Buhari ya yi wa Rivers, Wike
Na yi addu'ar kada a samu zaman lafiya a Nigeria saboda abinda Buhari ya yi wa Rivers, Wike. Hoto: @MobilePunch
Asali: Facebook

Wike ya ce jihar Rivers na fara da garkuwa da wasu laifuka a lokacin da ya kama aiki amma da ya nemi taimako wurin Shugaba Muhammadu Buhari, zai aka yi zargin yana kashe mambobin jam'iyyar APC.

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa ango rasuwa kwana ɗaya bayan ɗaurin aurensa

Don haka, sai ya yi addu'a Allah ya wanzar da rashin tsaro a sassar kasar har sai Shugaban kasa ya nemi afuwar jihar Rivers.

"A 2016 da muka karbi gwamnati, akwai kallubalen rashin tsaro a jihar. Ina ta ihu. Na ruga wurin gwamnatin tarayya 'ta bani dakaru na musamman kamar yadda na ji ana bawa wasu.' Suka ce 'a'.

"Wai ina kash yan APC. Sai na dawo gida na fada wa mutane na, 'kowa ya tseguna ya yi addu'a, ya roki Allah wannan rashin tsaron ya cigaba da wanzuwa a Nigeria kuma Nigeria za ta rasa yadda za ta yi.

"Kuma na fada musu 'idan ba ku nemi afuwar jihar Rivers ba, ba za ka taba ganin zaman lafiya ba.' Yanzu abinda ke faruwa a kasar nan kenan. Domin sunyi fatan wannan jihar ta durkushe.

"Gwamnoninsu da ke cewa muna kashe yan APC kuma yan PDP ne masu garkuwa, yanzu mene ke faruwa a Kaduna? Mene ke faruwa a Borno? Yau me ke faruwa a Ondo? Mene ke faruwa a sassan kasar? Amma akwai zaman lafiya a Rivers. Ina kallubalantarsu su ce sun taimaka min ko da ta rana daya ne. Babu wanda ya yarda ya taimake ni.

"A wannan jihar ne kawai gwamna ba zai iya zaben wanda zai zama kwamishinan yan sanda ba. Tun 2015 zuwa yanzu mun samu kwamishinoni 15 na yan sanda don ba su so Rivers ta cigaba."

A wani rahoton daban kunji cewa kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.

An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.

JNI, da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164