Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da matafiya a jihar Osun

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da matafiya a jihar Osun

- Wasu 'yan bindiga a jihar Osun sun yi awon gaba da wasu matafiya guda biyu A yankin Wasinmi.

- Mai magana da yawun 'yan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma yace an tura jami'an 'yan sanda a yankin da lamarin ya faru

- Matafiyan dake kan hanyar su ta zuwa yankin Ikire sun haɗu da ƙaddarar ne a yankin Wasinmi.

Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko suwane ne ba sun sace matafiya guda biyu da yammacin ranar Asabar a yankin da ake kira Wasinmi, jihar Osun.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, matafiyan da lamarin ya faru da su na kan hanyar su ne ta zuwa yankin Ikere, na jihar ta Osun.

KARANTA ANAN: Mukabala: Abduljabbar bai kai a yi masa gangami ba, in ji Sheikh Khalil

A lokacin da take bayani, mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Yemisi Opalola, ta tabbatar da sun sami labarin faruwar lamarin.

A cewar mai magana da yawun 'yan sandan, sun tura jami'an 'yan sanda yankin da lamarin ya faru don gudanar da bincike.

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da matafiya a jihar Osun
Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da matafiya a jihar Osun Hoto: @pmnewsnigeria
Source: Twitter

KARANTA ANAN: Mukabala: Abduljabbar bai kai a yi masa gangami ba, in ji Sheikh Khalil

Ta kuma kara da cewa, ya zuwa yanzun sun kama mutum uku da ake zargin suna da alaƙa da satar mutanen.

Sannan kuma zasu cigaba da bincike har sai sun kama waɗanda sukayi wannan aika-aika.

Kuma ta ƙara da cewa jami'an su na 'yan sanda sun bazama neman waɗanda aka sace a duk inda suke.

A wani labarin kuma Katin shaidar rigakafin korona zai zama sharaɗin fita daga Najeriya, in ji Boss Mustapha

Shugaban kwamitin yaki da kwayar cutar korona a Najeriya (PTF), Boss Mustapha, ya ce nan gaba katin shaidar yi wa mutum allurar rigakafin cutar zai zama wajibi ga matafiya kasashen waje

Mustapha wanda kuma shi ne sakataren Gwamnatin Tarayya, ya bayyana hakan ne a Fadar Shugaban Kasa a yau Asabar jim kadan bayan an yi wa shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo allurar rigakafin.

Ahmad Yusuf dan mtan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwanan nanAhmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Source: Legit.ng

Online view pixel