Ku daina tsokacin da zai zama kalubale ga tsaron kasa, Ganduje ga 'yan siyasa

Ku daina tsokacin da zai zama kalubale ga tsaron kasa, Ganduje ga 'yan siyasa

- Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje yayi kira ga 'yan siyasa da su guji tsokaci na zagon kasa ga tsaro

- Gwamnan ya bayyana goyon bayansa a kan hana jiragen sama bi ta jihar Zamfara don dakile ta'addanci

- Ya ce hakan zai shawo kan matsalar tsaro tare da dakile wawushe albarkatun kasar nan na zinari da ake yi

Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano yayi kira ga 'yan siyasa da su gujewa yin tsokacin da zai bata kokarin gwamnatin tarayya wurin tsaron kasar nan baki daya.

Ganduje ya bayyana goyon bayansa a kan haramtawa jiragen sama bi ta jihar Zamfara inda ya kwatanata hakan da tsari mai kyau, The Cable ta wallafa.

Gwamnan yayi wannan maganar ne ta bakin Muhammed Garba, kwamishinan yada labarai na jihar Kano a wata takarda da ya fitar a ranar Asabar.

KU KARANTA: Kamar El-Rufai, gwamnan Kogi yace ba zai yi sasanci da 'yan ta'adda ba

Ku daina tsokacin da zai zama kalubale ga tsaron kasa, Ganduje ga 'yan siyasa
Ku daina tsokacin da zai zama kalubale ga tsaron kasa, Ganduje ga 'yan siyasa. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: UGC

"'Yan siyasa su dakata tare da ganin yadda wannan tsarin yake aiki kafin su fara tsokacin da zai zamo kalubale ga kokarin gwamnati na tsare kasar nan," yace.

Gwamnan ya kara da cewa hana jiragen sama bi ta jihar zai dakile kaiwa 'yan ta'addan kayan bukata da kuma kwashe albarkatun kasar nan na zinari da ake yi a jihar.

"Lamarin tsaro yakamata a dube shi kafin siyasa. Ban ga wata siyasa ba a hana jiragen sama bi ta jihar Zamfara," yace.

“Saboda tsaro ne da kuma bayanan sirrin da aka samu na ta'addancin da ke faruwa a wurin."

Ganduje yace kasar nan tana bukatar hadin guiwar masu ruwa da tsaki wurin shawo kan matsalar garkuwa da mutane da ta'addanci.

Ya kara da kiran hadaka tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya domin gujewa duk abinda zai kara tsananta rashin tsaro a kasar nan.

KU KARANTA: Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana babban sirrinsa na haddar Al-Qur'ani

A wani labari na daban, tsohuwar matar tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigon jam'iyyar PDP, Femi Fani-Kayode, Precious Chikwendu ta maka tsohon mijinta a gaban kotu da bukatar karbar 'ya'yan da suka haifa.

Precious ta maka Fani-Kayode a gaban wata babban kotun tarayya dake Abuja inda take bukatar karbar 'ya'yanta hudu da suka haifa yayin da suke tare, amma a bar mahaifinsu ya dinga zuwa ganinsu, The Nation ta wallafa.

Matar mai son Fani-Kayode da duk wasu mukarrabansa su kiyayi kwace mata 'ya'yanta ta karfi da yaji, ta bukaci kotun da ta sa tsohon ministan ya dinga biyanta N3.438 miliyan duk wata domin kula da yaran tare da wasu kudi na daban domin karatunsu da sauran bukatunsu.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel