Da duminsa: Buhari ya bukaci a tsananta tsaro a iyakokin tudun kasar nan

Da duminsa: Buhari ya bukaci a tsananta tsaro a iyakokin tudun kasar nan

- Shugaban kasar Najeriya ya baiwa hukumar kula da shige da fice umarnin tsananta tsaro a dukkan iyakokin tudu na kasar nan

- Kamar yadda shugaban kasar ya sanar, hakan ce kadai mafita ga yadda rashin tsaro ya ta'azzara a fadin kasar nan

- Ya bukaci hukumomin tsaro da su zage damtse wurin sauke nauyinsu na baiwa rayuka da kadarori kariya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) da ta kara zage damtse wurin saka ido a iyakokin tudu na kasar nan saboda hauhawar rashin tsaron da ya addabi kasar nan.

A wata takarda da Femi Adesina, mai baiwa shugaban kasar shawara na musamman a fannin yada labarai, ya ce Buhari ya bada wannan umarnin ne a wani taro na yanar gizo da yayi a hukumar a Abuja.

Kamar yadda yace, dole ne dukkan hukumomin tsaro su dage wurin kula da rayuka da kadarorin jama'a domin inganta tsaron kasar nan.

KU KARANTA: Makuden kudaden fansa na karfafawa masu garkuwa da mutane guiwa, Buhari

Da duminsa: Buhari ya bukaci a tsananta tsaro a iyakokin tudun kasar nan
Da duminsa: Buhari ya bukaci a tsananta tsaro a iyakokin tudun kasar nan. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

Ya ce: "Abin farin ciki ne ganin yadda muka kara gaba a matakin tsaro na duniya kuma ina amfani da wannan damar wurin kira ga dukkan hukumomin tsaro da su zage damtse.

"Ina tabbatar mana da cewa wannan mulkin zai bada dukkan goyon bayan da ake bukata domin ayyukanku."

Shugaban kasan yayi kira ga NIS da ta hada kai da hukumomin tsaro na fadin duniya kamar INTERPOL domin tsare iyakokin kasar nan.

Ya kara da cewa: "A matsayinku na hukumomin tsaro, ina kira gareku da ku dage wurin sauke nauyinku na baiwa iyakokinmu kariya yayin da kuke tabbatar da cewa duk wani mai laifi bai samu sassauci a kasar nan ba."

KU KARANTA: Allah ya yi wa kanin Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi rasuwa

A wani labari na daban, tsohon dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC, Adamu Garba ya je kafar sada zumunta inda ya bayyana takaicinsa a kan yadda jama'a ke nuna ra'ayinsu dogaro da yankin mutum.

Garba ya kwatanta mutanen kudancin Najeriya da munafukai, ya ce basu iya kushe duk wani laifi da mutanen yankinsu suka yi amma su dinga kushe na arewa, Vanguard ta wallafa.

"Alamu suna nuna cewa muna da baiwar matsayi, mutunci da kuma arziki kuma muna da masu saka bama-bamai da alburusai a arewa," Garba yace.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel