Hadiza Gabon ta yi magana a kan soyayya, ta fadi abin da ya fi komai ba ta sha'awa a rayuwa

Hadiza Gabon ta yi magana a kan soyayya, ta fadi abin da ya fi komai ba ta sha'awa a rayuwa

- Hadiza Aliyu Gabon ta yi kira ga mutane su rika taimakon marasa hali

- ‘Yar wasar fim din ta ce soyayya ce za ta iya cire kiyayya cikin al’umma

- Tun a 2016 Hadiza Gabon ta kafa gidauniyarta, ta na tallafawa mabukata

Tauraruwar wasan kwaikwayon Kannywood, Hadiza Aliyu wanda aka fi sani da Hadiza Gabon, ta fadi abin da ya fi burge ta a rayuwar Duniya.

Fitacciyar ‘yar wasar Hausan ta ce ganin mutane su na nuna wa juna kauna, shi ne abin da ya fi burge ta.

Hadiza Gabon ta fada wa jaridar Daily Trust cewa daya daga cikin abubuwan da ke sa ta farin ciki, ya cire mata damu wa shi ne taimakon marasa karfi.

Ta ce: "Ta ya ya mutum zai rika tunanin cewa lafiya kalau komai yake tafiya saboda su ta yi masu kyau, sai su manta da wadanda su ke kwana da yunwa?"

KU KARANTA: Hotunan Nafisa Abdullahi da su ka gigita shafukan yanar gizo

‘Yar wasar fim din ta ce: “Ya na da muhimmanci a sani cewa za a dade ba manta da ‘dan kokarin kirkin da ka ke yi wanda zai canza rayuwar mutane ba.”

“Mu rika yin bakin kokarinmu wajen canza rayuwar talakawa da mabuka a cikinmu.” Inji Gabon.

Idan za a tuna shekaru kusan biyar da su ka wuce kenan da ‘Yar wasar fim din Hausar ta kafa gidauniyar HAG da nufin inganta rayuwar masu karamin karfi.

Tun daga nan Gabon ta bude kofa, ta yi abin da ba a taba gani ba a Kannywood, ta na taimakon wadanda ba su da hanyar samun kiwon lafiya da samun ilmi.

KU KARANTA: Babur ya kashe daya daga cikin ‘Ya ‘yan Dahiru Mangal a Katsina

Hadiza Gabon ta yi magana a kan soyayya, ta fadi abin da ya fi komai ba ta sha'awa a rayuwa
Jaruma Hadiza Gabon Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Ina tsananin kiran ga mutane su rungumi kaunar juna, shi ne lokacin da mu ke nuna wa juna soyayya da kula. Idan aka yi haka, kiyayya za ta bar al’ummar mu.”

“Jama’a za su yi nasara idan akwai soyayya, kauna da taimakon juna da ta bayyana a ko ina.” inji ta.

Kwanaki kun ji labarin yadda Hadiza Aliyu Gabon ta yi wa wani dattijo da ya nuna yana kaunarta gagarumar kyauta. Gabon ta ba wannan Bawan Allah kudi har N200, 000.

An rahoto wannan mutum ya na mai cewa: “Alhamdulillah, Ma shaa Allah, Hajiya Hadiza na ga sako nagode Allah ya saka da alkhairi, ubangiji Allah ya bar zumunci..."

Har ila yau, wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Instagram mai suna Kabir Idris Kura ya wallafa bidiyon wani masallaci da Tauraruwa Gabon ta gina.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng