Sabbin zafafan hotunan Nafisa Abdullahi kusa da dankareriyar motarta

Sabbin zafafan hotunan Nafisa Abdullahi kusa da dankareriyar motarta

- Fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisat Abdullahi ta saki wasu zafafan hotunanta

- An gano jarumar wacce tauraronta ke ci gaba da haskawa a gaban wata dankareriyar motarta

- A yan baya-bayan nan dai jarumar bata cika fitowa a fina-finan Hausa ba

Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Nafisa Abdullahi wacce aka fi sani da ‘Sai wata rana’ ta saki wasu sabbin zafafan hotunanta.

An gano fitacciyar jarumar tsaye a gaban dankareriyar motarta kirar Mercedes-Benz.

Nafisa ta saki sabbin hotunan ne a shafinta na Instagram a ranar Asabar, 3 ga watan Oktoba, sanye da gilashi cikin salo kala-kala.

Sabbin zafafan hotunan Nafisa Abdullahi kusa da dankareriyar motarta
Sabbin zafafan hotunan Nafisa Abdullahi kusa da dankareriyar motarta Hoto: nafeesat_official
Asali: Instagram

Jarumar dai a iya cewa ta yi batan dabo a Kannywood. Sai dai masoyan ta na ci gaba da dakon ganin ta a nan gaba.

KU KARANTA KUMA: An gano labarin matar da ta kashe ƴaƴanta 2 a Kano, da dalilin da ya sa ta kashe su

Har ila yau, Nafisa na ci gaba da dukan hankulan masoyan ta a cikin fim ɗin nan na Arewa24 mai dogon zango, 'Labari Na', inda ta ke taka rawa kamar yadda aka tsara.

KU KARANTA KUMA: Bidiyon matar aure dauke da goyo tana fenti don samun abun ciyar da 'ya'yanta

A wani labarin kuma, Dino Melaye, tsohon sanata da ya taba wakiltar yankin Kogi na yamma, ya darzo sabuwar motar kirar Lamborghini Aventador Roadstar.

Tunde Ednut ne ya wallafa hotuna tare da bidiyon motar alfarmar a shafinsa a ranar Asabar da ta gabata.

Fitaccen sananne a shafukan sada zumuntar ya wallafa hoton tsohon dan majalisar yana tuka motarsa mai darajar dala miliyan daya wanda yayi daidai da N460,000,000.

"Sanata Dino Melaye ya siya sabuwar mota kirar Lamborghini Aventandor Roadstar kirar 2020. Kamfanin sun fitar da ita ne a bikin cikarsu shekaru 50. Wannan tana daya daga cikin guda 100 da kamfanin suka yi su a kan dala miliyan 1," ya wallafa a Instagram.

A watan Maris da ya gabata, tsohon sanatan ya koka da tarin dawainiyar da ke kansa duk da hotunan katafaren gidansa da ya wallafa nasa a kasar ketare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng