Mashahurin Attajirin Arewacin Najeriya, Dahiru Mangal ya yi babban rashin ‘da

Mashahurin Attajirin Arewacin Najeriya, Dahiru Mangal ya yi babban rashin ‘da

- Nura Dahiru Mangal ya yi hadarin babur ya rasu a garin Katsina

- Marigayin ya na cikin ‘Ya ‘yan Attajirin Katsina, Dahiru Mangal

- A yau Alhamis za ayi wa Nura sutura, a birne shi a Kofar Kwaya

Rahotanni sun zo mana cewa Nura, daya daga cikin ‘ya ‘yan fitaccen ‘dan kasuwan Najeriya, Dahiru Barau Mangal, ya mutu bayan ya yi hadari.

Nura Dahiru Mangal ya yi hadari ne a kan babur yayin da yake tuki a kan hanyar Dutsinma, Katsina.

Kamar yadda Daily Trust ta bayyana jiya, Nura Dahiru Mangal ya gamu da ajalinsa ne bayan ya wuce makarantar koyon aiki ta Hassan Usman Katsina.

Nan take aka garzaya da shi zuwa babban asibitin gwamnati na jihar Katsina wanda bai da nisa da inda wannan mummunan hadarin ya auku jiya da yamma.

KU KARANTA: Duk ranar Duniya, sai an samu akalla Sojan Najeriya 1 da ya ajiye aiki

Ko da aka isa asibiti a ranar Laraba, 3 ga watan Maris, 2021, sai likitoci su ka tabbatar cewa ya cika.

Wata majiya daga cikin gidan Dahiru Mangal, ta bayyana cewa za ayi wa marigayin sallar jana’iza a birne shi ne a yau Alhamis da karfe 10:00 na safe.

Za ayi jana’izar Nura Dahiru Mangal a masallacin Mangal wanda ke unguwar Kofar Kwaya, Katsina.

Marigayi Nura Dahiru Mangal ya rasu ya na da shekaru 30 a Duniya. Ya yi karatu a Katsina da ketare, ya yi karatun digiri a jam’ar Manchester da ke Birtaniya.

KU KARANTA: Tsofaffin ‘Yan bindiga sun taka rawar gani wajen kubuto da ‘Daliban Zamfara

Mashahurin Attajirin Arewacin Najeriya, Dahiru Mangal ya yi babban rashin ‘da
Nura, 'Dan Dahiru Barau Mangal Hoto: legit.ng
Asali: Original

Wani Bawan Allah wanda ya san wannan matashi ya rubuta a shafinsa ya na jimami, ya ce: "Allah ya jikan Nura Mangal. Allah ya sa Aljannah ce makomarsa.”

A shekarun baya Yusuf Buhari wanda ‘Da ne wurin Shugaban Kasar Najeriya yayi irin wannan hadari a babur, amma da yake da sauran kwana a gaba, ya yi rai.

Sai da ta kai yaron Shugaban Kasar bai cikin hayyacinsa, aka kwantar da shi a bangaren ICU na 'yan rai-hannun Allah a sashen wani asibitin kudi da aka duba sa.

Yusuf Buhari shi kadai 'da namiji da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mallaka.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel