Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa dan majalisar wakilai, Yuguda Kila, rasuwa
- Allah ya yi wa dan majalisa mai wakiltar mazabar Gwaram, Yuguda Hassan Kila, rasuwa
- Ya rasu ne yana da shekaru 70 a duniya bayan wata kwarya-kwaryar rashin lafiya da yayi
- Dan majalisar ya rike kujerar shugaban kwastam kafin ya koma harkar siyasa dumu-dumu
Dan majalisa mai wakiltar mazabar Gwaram, Yuguda Hassan Kila, ya rasu a ranar Alhamis bayan wata kwarya-kwaryar rashin lafiya da yayi har aka kwantar dashi a wani asibitin tarayya dake babban birnin tarayya Abuja.
Kila ya rasu yana da shekaru 70 a duniya. Shine shugaban kwamitin kwastam a majalisar wakilan Najeriya.
Tsohon shugaban kwastam din, wanda daga baya ya koma harkar siyasa ya yi karatun firamarensa ne a Kila Primary School, daga baya ya koma Igbo Union Grammar School dake Kano.
KU KARANTA: Rashin tsaro: PDP na zargin APC da kitsa yadda za ta kwace jihar Zamfara

Source: Twitter
Ya kuma yi karatu a kwalejin Barewa dake Zaria daga baya ya koma Kwalejin Palm Beaches dake kudancin Palm Beach a Florida, kasar Amurka.
An zabe shi ne a 2015 a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Gwaram karkashin jam'iyyar APC.
An kara zabensa a kan wannan kujerar a zaben 2019 da aka yi, inda ya cigaba da zama a kujerarsa.
KU KARANTA: Abinda yasa ni da takwarana na jihar Bauchi muka ajiye takubbanmu, Ortom
A wani labari na daban, Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara ya ce 'yammatan Jangebe sun bayyana cewa maigadinsu na makaranta yana daga cikin wadanda aka hada kai dasu aka sacesu.
A ranar Laraba da ta gabata ne Matawalle ya bayyana a shirin siyasarmu a yau na gidan Talabijin na Channels.
Sama da dalibai 270 ne aka sace a makarantar gwamnati da ke garin jangebe na karamar hukumar Talata-Mafara da ke Zamfara a watan Fabrairu. An sako su a ranar Talata.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng