Gwamnoni zasu tattauna kan yadda za'a raba rigakafin corona

Gwamnoni zasu tattauna kan yadda za'a raba rigakafin corona

- Gwamnonin kasar nan zasu shiga tattaunawa da junansu a kan yadda za'a gudanar da allurar rigakafin cutar corona

- Babban makasudin taron shine yadda za'a rarraba kashin farko na rigakafin kamar yadda me magana da yawun kungiyar ya sanar

- An tura ma kowa da katin gayyata, kuma za'a zaman ne ta hanyar amfani da fasahar zamani (Virtually)

Gwamnonin jihohi 36 sun shirya zama ranar alhamis karkashin jagorancin kungiyarsu don tattaunawa kan yadda zasu bullo ma allurar rigafin cutar corona.

A wani sako da kungiyar gwamnonin ta fitar ranar Laraba, ta hannun mai yada labaran kungiyar, Mr Bello-Barkindo yace, za'a yi taron ne ta yanar gizo.

KARANTA ANAN: Mashahurin Attajirin Arewacin Najeriya, Dahiru Mangal ya yi babban rashin ‘da

A cewarsa: "Taron da ya kunshi abu daya wato yadda za'a rarraba rigakafin cutar corona a dukkan fadin kasar."

Jaridar Vanguard ta ruwaito Bello-Barkindo na cewa: an aika ma kowanne gwamna da gayyar taron, kuma za'a fara da misalin karfe 5, na yamma.

Gwamnoni zasu tattauna kan yadda za'a raba riga kafin corona
Gwamnoni zasu tattauna kan yadda za'a raba riga kafin corona Hoto: @NGFsecritariat
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Makiyaya 2 da suka bata sun gamu da ajalinsu a Zangon Kataf

A ranar Talata da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta tabbatar da isowar rigafin kimanin 3.9 miliyan.

Shirin da hukumar lafiya ta duniya ta bullo dashi na (COVAX) tare da hadin gwuiwar wasu kungiyoyi ne suka turo da rigakafin Nigeria.

A wani labarin kuma Allah ya yi wa ango rasuwa kwana ɗaya bayan ɗaurin aurensa

Kamar yadda abokansa suka wallafa a dandalin sada zumunta, sunce mutuwar kawai ta zo ne nan take

Mutane da dama sun yi masa addu'ar Allah ya jikansa ya bawa matarsa da iyalansa hakurin jure rashinsa.

Ahmad Yusuf dan mtan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262