Yanzu-Yanzu: An tsige mataimakin kakakin majalisar wakilan jihar Ogun

Yanzu-Yanzu: An tsige mataimakin kakakin majalisar wakilan jihar Ogun

- Ranar Litinin din data gaba ta Shugaban majilisar jihar ya nada kwamitin bincike akan Kadiri

- Satin daya wuce 'yan majisu 20 suka kada kuri'ar amincewa da tsige shi.

- Rahoto ya bayyana an tsige shi a yau Alhamis

A yau, Alhamis, majalisar wakilan jihar Ogun ta bayyana tsige mataimakin kakakinta , Hon Dare Kadiri bisa dalilin rashin bin dokoki.

Hon. Dare Kadire na wakiltar mazabar arewacin Ijebu 2.

KARANTA ANAN: Abdul-Jabbar: JNI ta ce ba za ta hallarci muqalabar da gwamnatin Kano ta shirya ba

A kalla 'yan majalisu 20 ne suka amince da tsige mataimakin nasu a satin daya gabata.

KARANTA ANAN: Gwamnatin Zamfara ta saka dokar hana fita a Jangebe sakamakon tarzoma

A ranar Litinin din data gabata ne shugaban majalisar ya nada kwamitin mutum biyar don ya yi bincike akan zargin da ake ma Kadire.

Daga cikin dalilan da suka sa aka tsige shi daga mukaminsa shine "Rashin da'a."

Jaridar Vanguard ta wallafa tsige mataimakin kakakin majalisar wakilan a yau

Yanzu-Yanzu: An tsige mataimakin kakakin majalisar wakilan jihar Ogun
Yanzu-Yanzu: An tsige mataimakin kakakin majalisar wakilan jihar Ogun Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

A wani labarin na daban Bincike ya fallasa yadda masu hakar gwal ta bayan-fage su ke hura wutan rashin tsaro

Ana hasashen cewa 80% na gwal din da ake hako wa a Arewa maso yamma ya na zuwa ne ta baraunyiar hanya, ba tare da sanin hukumomi ba.

Bincike ya nuna akwai alaka tsakanin hake-haken gwal da rikicin da ake yi

Ahmad Yusuf Muhammad Dabai dan jihar Katsina ne mai burin zama shahararren dan jarida.

za'a iya bibiyarsa a shafin sada zumunta na instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel