Gwamnatin Zamfara ta saka dokar hana fita a Jangebe sakamakon tarzoma

Gwamnatin Zamfara ta saka dokar hana fita a Jangebe sakamakon tarzoma

- Gwamnatin jihar Zamfara ta saka dokar hana fita a garin Jangebe da ke jihar Zamfara

- Hakan ya biyo bayan zanga-zangar da matasan garin suka yi ne da ya rikide ya zama tarzoma

- Gwamnatin har ila yau ta kuma bada umurnin rufe dukkan kasuwannin da ke Jangebe zuwa wani lokaci nan gaba

Gwamnatin Jihar Zamfara ta saka dokar hana fita daga yamma har asuba a garin Jangebe sakamakon tarzomar da ta faru bayan sakin daliban makarantar GGSS Jangebe da ke karamar hukumar Talata-Mafara, The Cable ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma rufe kasuwanni garin domin hana ayyukan da ka iya 'taimakawa ko tallafawa' yan bindiga.

Gwamnatin Zamfara ta saka dokar hana fita a Jangebe sakamakon tarzoma
Gwamnatin Zamfara ta saka dokar hana fita a Jangebe sakamakon tarzoma. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa ango rasuwa kwana ɗaya bayan ɗaurin aurensa

Idan za ku iya tunawa dai an kashe mutum daya yayin da biyu suka jikkata sakamakon tarzoma da ta barke tsakanin jami'an tsaro da wasu matasa a garin.

An ce matasan sun yi zanga-zanga ne a lokacin da jami'an gwamnatin jihar suka zo garin domin mika daliban da aka sace ga yan iyayensu.

Matasan sun nuna bacin ransu ga gwamnatin bisa satar mutane da kashe-kashe da ake yi a jihar.

Sai dai, rikici ya barke a lokacin da aka hana matasan su kai ga jami'an gwamnatin.

Kwamishinan labarai na jihar Zamfara, Suleiman Anka, ya ce dokar hana fitar za ta fara aiki daga ranar Laraba.

KU KARANTA: Sadiq Daba: Tsohon ɗan jarida kuma ɗan wasan kwaikwayo ya rasu

"Sakamakon rashin da'a da ya faru a garin Jangebe bayan da aka dawo da daliban da aka sace, gwamnatin Zamfara ta amince da saka dokar hana fita daga dare har asuba a garin Jangebe," in ji Anka.

"An saka dokar ne don tabbatar da zaman lafiya.

"Kazalika, an gano cewa akwai hujja da ke nuna cin kasuwanni a garin da garuruwan da ke makwabtaka da shi na taimakawa yan bindiga. Don haka an rufe kasuwanni har zuwa wani lokaci nan gaba."

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel