Gwamna Zulum ya fadawa Gwamnati dabaru 2 da za a bi, a kawo kashen 'Yan Boko Haram

Gwamna Zulum ya fadawa Gwamnati dabaru 2 da za a bi, a kawo kashen 'Yan Boko Haram

- Farfesa Babagana Umara Zulum ya sake bada shawara a kan yakin Boko Haram

- Gwamnan na jihar Borno ya dage a kan a dauko hayar sojoji daga kasashen waje

- Zulum ya ce sai an nemi gudumuwa daga waje, sannan za a gama da Boko Haram

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi magana a wajen taron gwamnonin Arewa maso gabas da aka yi a jihar Bauchi jiya.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa taron ya samu halartar gwamnoni; Bala Mohammed, Ahmadu Fintiri, Muhammad Yahaya da kuma Darius Ishaku.

Babagana Umara Zulum wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin, ya ce akwai bukatar hada karfi da karfe wajen kawo karshen matsalar ta’addanci.

KU KARANTA: Wasu 'Yan ta'addan Boko Haram Kiristoci ne - Gwamna Zulum

“Har ila yau dai, ina so in yi amfani da wannan dama, in yi kira ga gwamnatin tarayya, ta nemi gudumuwar makwabtanmu, musamman Chad da Nijar, da nufin yin hadin-gwiwa da zai kawo yiwuwar ganin karshen wannan rikici.” Inji gwamnan.

Zulum ya kuma ce: “Bayan haka, gwamnatin tarayya ta duba yiwuwar dauko hayar kwararrun sojoji daga waje domin a kawo karshen ta’addancin nan.”

Ya ce: “Idan mu na so mu kawo karshen yakin nan, dole mu yi da gaske. Sai mun nemi taimako daga kasashen waje; sai mun tabbatar an kawo sojojin haya.”

Zulum ya yaba wa jami’an tsaro, ya ce: “Hakika, ba za ayi shakkar jajircewar sojojinmu da kokarin ganin an samu nasara a wannan yaki daga dakarunmu ba.

KU KARANTA: Barnar da tubabbun ƴan ta'addan Boko Haram su ke yi

Gwamna Zulum ya fadawa Gwamnati dabaru 2 da za a bi, a kawo kashen 'Yan Boko Haram
Gwamnonin Arewa maso gabas a taro
Asali: Twitter

Amma a cewar gwamnan, ya kamata sababbin hafsoshin sojoji su kawo sababbin dabarun yaki.

Ba wannan ne karon farko da Babagana Umara Zulum ya bada shawarar a dauko sojoji daga ketare su taya Najeriya yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram ba.

Gwamnatin Goodluck Jonathan ce ta dauko hayar sojoji daga kasashen waje wanda su ka taya dakarun Najeriya yakar ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram.

Daga baya shugaba Muhammadu Buhari ya sallami sojojin hayan, ya ce abin kunya ne. Farfesa Zulum ya na ganin ana bukatar wadannan jami’ai da aka sallama.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel