Cikin kwana 1, Mutum 2.3 miliyan sun yi rijistan yi musu Rigakafin Cutar Corona, Gwamnati

Cikin kwana 1, Mutum 2.3 miliyan sun yi rijistan yi musu Rigakafin Cutar Corona, Gwamnati

- Mutum Miliyan 2.3 sun amince a yi musu allurar rigakafin cutar covid19

- Shugaban hukumar lafiya yace babu wasu tsirarun mutane da aka ware ma allura.

- Zamu fi bawa ma'aikatan lafiya muhimmanci

A ranar Laraba hukumar lafiya ta kasa ta kore duk wata fargaba da ke nuna cewa 'yan nigeria baza su yarda amusu allurar rigafin cutar corona ba.Ya zuwa yanzu mutane 2.3 miliyan suka amince amusu rigakafin.

A lokacin zantawarsa da channels TV a shirin Sunrise daily, shugaban hukumar kula da lafiya ta kasa kuma kwararren likita yace:

"Zan iya cewa abu ne mai dadi matuka zuwan rigakafin Najeriya. Na san mutane na dar-dar, amma muna iya kokarin mu."

"Kar kaso kaga yadda 'yan Nigeria ke nuna matukar sha'awarsu wajen bukatar ayi musu wannan rigakafin."

Dr. ya kara da cewa: "Daga tsakiyar daren Litinin da muka kaddamar da rijistar amincewa ta yanar gizo, Mun sami mutum 2.3 miliyan da sukayi rejista don karbar rigakafin."

Kuma mutane na cigaba dayin rejista.

Mutum Miliyan 2.3 Sun Amince A Musu Rigakafin Cutar Corona Cikin Awa 24
Mutum Miliyan 2.3 Sun Amince A Musu Rigakafin Cutar Corona Cikin Awa 24 Hoto: Facebook/Nigeria centre for disease control
Source: Facebook

KARANTA ANAN: Wata sabuwa: Sowore a kotu tare da wani mai tsaron da ba a saba gani ba

Shugaban ya cigaba da cewa: "Isowar kashin farko na allurar rigakafin babban ginshiki ne wajen yaki da cutar data harbi sama da mutum 150,000 a kasar."

Dr Faisal yace akwai sauran aiki a gaban mu: "Mun dauki aikin da muhimmanci shiyasa zamu zage dantse muyi aiki tukuru."

Dr. Faisal ya bayyanar da cewa: "Eh, rigakafin ta iso, amma akwai aiki sosai daya fi na baya da zamuyi don tabbatar da anyiwa yan kasa rigakafin ta hanya mafi sauki, hanyar da baza'a sha wahala ba."

Yace hukumarsa tayi tsarin yadda za'a rarraba maganin kuma tsarin na gaban hukumar kula da harkokin abinci data kwayoyi ta kasa (NAFDAC).

KARANTA ANAN: Yanzu-yanzu: An bindige jami'an 'yan sanda har lahira a Cross Rivers

"Muna jiran (NAFDAC) ne yanzun, muna jin zasu yi duk binciken daya kamata kuma da zaran sun gama zamu rarraba allaurar"

Shugaban (NPHCDA) ya yi watsi da duk wata jita-jitar da ake yadawa cewa an ware allurar rigafin ga wasu manya,

Ya jaddada cewa za'afi bada muhimmanci ga ma'aikatan lafiya da makamantansu wajen gudanar da rigakafin.

"Inaso in kara tabbatar muku da cewa bamu bayar da wannan allurar rigakafin ga wasu masu kudi ko mutanen dake birane ba, Shugaban kasa ya yi bayani mai gamsarwa a kan Haka"

Mataimakin shugaban kasa ma ya kara bayani kuma shugaban kwamitin yaki cutar ya kara bayani a lokacin da yake jawabi da kafofin yada labari.

Ya yi bayani mai gamsar wa akan wadan da za'a fi bama muhimmanci, kuma zan kara maimaitawa

"Mutanen da za'a fi bawa muhimmanci sune wadanda suka bada rayuwarsu wajen kula da yan Nigeria da suka harbu da cutar a shekarar data gabata. Saboda haka na farko sune ma'aikatan lafiya" faisal ya fada

"A ranar jumu'a zamu kaddamar da allurar rigakafin, zamu rarrabata zuwa wuraren da aka tanazar da kuma asibitoci.

Sannan zamu bada muhimmanci ga jami'an lafiya don sune kan gaba. Sannan zamuyi ma wadanda suka fara bukata" inji Faisal

Bayan ma'aikatan lafiya, ya bayyana cewa za'ayi ma wasu shuwagabanni allurar wanda hakan zai jawo hankalin wasu.

Daga karshe yace "Zamu yi wa manyan shuwagabanni kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa.

Da kuma wasu mutane da suka yarda a yi musu a bayyane don hakan yaba wasu karfin gwuiwar zuwa a yi musu allurar"

A wani labarin kuma Miyagun sun bindige Rabi’u Amarawa bayan sun karbi kudin fansarsa

Yan uwan Alhaji Rabi’u Amarawa sun ba ‘Yan bindigan kudi har N5m

Miyagun sun bindige Rabi’u Amarawa bayan sun karbi kudin fansarsa

Ahmad Yusuf dalibi ne mai neman ilimi, yayi karatu a Kano University of science and technology wudil.

Za a iya bibiyarsa a Facebook facebook/Ahmad Yusuf Muhammad

Source: Legit.ng

Online view pixel