Miyagu sun yi rashin imani, sun karbi Miliyan 5, kuma sun bindige ‘Dan kasuwa a Sokoto

Miyagu sun yi rashin imani, sun karbi Miliyan 5, kuma sun bindige ‘Dan kasuwa a Sokoto

- ‘Yan bindiga sun hallaka wani ‘Dan kasuwan da aka sace a Garin Illela

- Miyagun sun bindige Rabi’u Amarawa bayan sun karbi kudin fansarsa

- ‘Yan uwan Alhaji Rabi’u Amarawa sun ba ‘Yan bindigan kudi har N5m

Rahotanni daga Daily Trust su na tabbatar da cewa ‘dan kasuwan nan da aka sace a Sokoto, Alhaji Rabi’u Amarawa, ya gamu da ajalinsa a hannun ‘yan bindiga.

‘Yan bindigan sun hallaka wannan Attajiri bayan sun karbi Naira miliyan 5 a matsayin kudin fansarsa. Amma wannan bai hana su bindige shi har lahira ba.

Wata majiya daga dangin ‘dan kasuwan ta shaida wa ‘yan jarida cewa an kashe Rabi’u Amarawa ne bayan ‘yan uwansa sun biya kudi N5m domin a fito da shi.

‘Yanuwan wannan Bawan Allah sun ce sun samu labarin ‘yan bindiga sun kashe Alhaji Amarawa. Abin da ya rage shi ne ayi kokari a nemo gawarsa a daji.

KU KARANTA: Kudin fansa na karfafa wa 'Yan bindiga gwiwa - Buhari

“An sanar da mu labarin mutuwarsa daga majiya mai karfi. Mutane sun shiga jeji, su na neman gawansa.”

Da aka tuntubi jami’in da ke magana da yawun bakin rundunar ‘yan sanda na jihar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar, ya ce bai san da wannan maganar ba tukuna.

ASP Sanusi Abubakar yake cewa: “Amma zan tuntubi mutanena, sannan in dawo gare ku.”

Wannan mummunan lamari ya na zuwa ne bayan kwanaki kadan da aka sace wannan attajiri da ke garin Illela Amarawa, a karamar hukumar Illela, jihar Sokoto.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun addabi Kaduna, sun kashe mutane 6

Miyagu sun yi rashin imani, sun cinye kudin fansar Miliyan 5, sun bindige ‘Dan kasuwa a Sokoto
Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal Hoto: @AWTambuwal
Asali: Twitter

‘Yan bindiga sun zo har gida sun dauke Rabi’u Amarawa da kimanin karfe 2:00 na tsakar dare a ranar Litinin, daga nan iyali da ‘yanuwa ba su sake ganin fuskarsa ba.

A jiya kun ji cewa akalla mutane 12 sun mutu wajen ceto wannan mai kudin da 'yan bindiga su ka yi garkuwa da shi a karamar hukumar Illela da ke cikin jihar Sokoto.

A lokacin da aka dauke shi, iyalan wannan mutum sun yi maza sun sanar da jami’an tsaron sa-kai game da abin da ya faru, inda su kuma su ka yi yunkurin su ceto shi.

Wannan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12 a hannun 'yan bindiga, har da 'danuwan marigayin.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng