Ba a biya kudin fansa wajen fito da ‘Yan makarantar Jangebe ba inji Gwamnan Zamfara
- Gwamnan jihar Zamfara ya bayyana yadda aka bi aka ceto Daliban GSS Jengebe
- Bello Matawalle ya ce tsofaffin ‘Yan bindiga su ka taimaka aka kubuto da yaran
- Dalibai 279 aka kubutar bayan sun shafe kwanaki hudu a hannun ‘Yan bindiga
Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle ya bayyana yadda aka bi aka ceto ‘daliban makarantar mata ta Jengebe da aka sace a makon jiya.
Mai girma gwamna Muhammad Bello Matawalle ya ce tsofaffin ‘yan bindigan da su ka tuba ne su ka yi uwa da makarbiya wajen fito da wadannan yaran.
A cewar gwamnan na jihar Zamfara, ko sisi gwamnati ba ta ba ‘yan bindigar da su ka dauke ‘yan matan ba.
Gwamna Bello Matawalle wanda ya yi wa ‘yan bindiga afuwa, ya ce tubabban masu laifin da ke jihar ne su ka ceto wadannan ‘dalibai daga hannun miyagu.
KU KARANTA: Masu satar mutane sun yi cinikin kudin fansar Biliyan 10 a 2021
Gwamnan ya bayyana wannan ne a lokacin da BBC Hausa ta yi hira da shi da safiyar ranar Talata, 2 ga watan Maris, 2021, bayan an kubuto da duka ‘yan matan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bello Matawalle ya ce wasu ‘yan bindiga su kusan 30 da su ka tuba, su ka ajiye makaman yaki ne su ka taimaka wa gwamnati wajen ceto ‘daliban nan su 279.
Kamar yadda gwamna Matawalle ya yi bayani, duka yaran da aka ceto su na cikin koshin lafiya. A lokacin ya yi alkawari za a hada kowa da iyayensa daga baya.
Har ila yau, gwamnan ya karyata rade-radin da ake yi na cewa wasu daga cikin ‘daliban da aka sace sun yi batan-dabo ko su na nan a hannun ‘yan bindigan.
KU KARANTA: Mun ci duka a hannun wadanda suka sace mu - Daliban Kagara
Matawalle ya ce tun asali ‘dalibai 279 aka dauke daga wannan makarantar gwamnati kamar yadda rajista ta nuna, akasin rahoton da aka ji na cewa su 217 aka sace.
Watanni biyu da su ka wuce ne 'yan bindiga su ka sace wasu 'yan makaranta a jihar Katsina.
Daga baya kungiyar Boko Haram ta fito ta na bada sanar cewa ita ce ta sace wadannan dalibai fiye da 300 daga makarantar sakandaren kimiyya da ke Kankara.
Kamar yadda HumAngle ta rawaito, gwamnatin Katsina ta ce 'yan bindiga ne su ka dauke yaran.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng