A wata 2 cikin 2021, ‘Yan bindiga sun tashi da N10bn ta hanyar garkuwa da mutum 720

A wata 2 cikin 2021, ‘Yan bindiga sun tashi da N10bn ta hanyar garkuwa da mutum 720

- Bincike ya nuna cewa an yi awon gaba da mutane sama da 720 a 2021

- Masu garkuwa da mutane sun samu Naira biliyan 10 a shekarar bana

- Yanzu Arewa ya fi kaurin suna da matsalar satar mutane a kasar nan

Akalla ba a kasara ba, mutane 720 aka sace, aka yi garkuwa da su a shekarar nan a Najeriya, binciken da jaridar Vanguard ta gudanar ya nuna haka.

Sunday Vanguard ta ce biciken da ta yi, ya nuna babu inda ake fama da matsalar garkuwa da mutane a kaf Najeriya kamar babban birnin tarayya Abuja.

A wannan shekarar, an samu labarin mutane fiye da 400 da aka dauke a Arewa maso yamma, sai yankin Arewa ta tsakiya, inda aka sace mutane kusan 250.

Duk da haka ana ganin cewa akwai mutane da-dama da aka dauke a jihohi musamman irinsu Neja, Sokoto, Zamfara da Katsina, ba tare da an samu labari ba.

KU KARANTA: Buhari ya bada umurnin ƙaddamar da yaƙi da masu garkuwa da mutane

Yankunan da ake da karancin wannan matsala su ne Kudu maso gabas da kuma Kudu maso kudu. Idan aka tattaro adadin, za a samu an dauke mutane 720.

Ana kiyasin cewa kudin da wadannan miyagu su ka samu a shekarar nan ya haura Naira Biliyan 10.

Manyan hanyoyin da masu garkuwa da mutane su ka addaba sun hada da ta Benin-Ore, Benin-Auchi-Okene, Keffi-Akwanga, da kuma titin Akure-Owo.

Hanyoyin Arewa da su ka zama tarkon ‘yan bindiga su ne Abuja-Lokoja, Zaria-Sokoto-Gusau, Bauchi-Tafawa-Balewa, Wukari-Takum da Minna-Kotongora.

KU KARANTA: 'Yan siyasa na da hannu a rikicin da ake yi - Matawalle

A wata 2 cikin 2020, ‘Yan bindiga sun tashi da N10bn ta hanyar garkuwa da mutum 720
Sufetan 'Yan Sandan Najeriya Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Alkaluman SBM sun ce an biya fam Dala miliyan $18.3 da Naira biliyan 7 domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su tsakanin Yunin 2011 zuwa shekarar 2020.

A irinsu Shika/Giwa a titin Zaria-Gusau-Sokoto da kuma yankin Abaji, a kan saida mutumin da aka sace ga tantiran masu garkuwa domin su yi kudi sosai da shi.

Dazu kun ji cewa Rundunar Najeriya ta na asarar jami'anta. Majalisar wakilai ta ce sojojin kasa fiye da 380 su ka ajiye aikinsu, su ka yi gaba a shekarar da ta gabata.

Kwamitin harkar sojojin kasa a majalisar wakilan tarayya ya ce binciken da ya yi, ya nuna sojoji 386 suka ajiye aiki saboda ganin damarsu ko larurar rashin lafiya.

Sojoji 356 sun yi sallama da gidan sojan bayan sha’awar aikin ya fita a ransu. Sannan wasu jami’ai 24 sun ajiye aikinsu, bayan sun samu sarautar gargajiya a gida.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng