Farashin Rago ya kai N1m a Legas sakamakon yajin aikin kai kayan abinci kudu

Farashin Rago ya kai N1m a Legas sakamakon yajin aikin kai kayan abinci kudu

- Farashin kayan abinci da dabobbi sunyi tashin gwauron zabi a jihohin kudu sakamakon yajin aikin kungiyar masu kayan abinci da dabobbi

- Saboda tsanantar lamarin har ta kai ga an siya rago kan kudi Naira miliyan 1 da kuma N800,000 a Legas

- Kungiyar masu kayan abincin da dabobbi ta shiga yajin aikin ne sakamakon barnar da aka yi wa yan arewa yayin rikicin Shasha a jihar Oyo

- Kungiyar ta na neman a biya ta fansar Naira biliyan 4.7 sannan tana bukatar a dauki matakan kare rayuka da dukiyoyin yayanta

Yajin aikin da kungiyar masu kayan abinci da dabbobi ta Nigeria ya janyo farashin dabbobi ya yi tashin gwauron zabo a jihar Legas da wasu jihohin kudu maso yamma.

Idan ba a manta ba, kungiyar ta masu kayan abinci da dabobi a ranar Alhamis ta fara yajin aiki, inda ta rufe iyakokin da ke tsakanin Arewa da Kudu don nuna kin amincewarsu da lalata kayan yan arewa yayin rikicin kasuwar Shasa a jihar Oyo.

Kudin rago ya kai miliyan daya a Legas sakamakon yajin aikin yan
Kudin rago ya kai miliyan daya a Legas sakamakon yajin aikin yan. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun yi barazanar kashe mu, su soya namar mu su cinye, Ɗalibar Jangebe

Kungiyar tana neman a biya ta diyyar Naira biliyan 4.7.

Kimanin kwanaki biyar da fara yajin aikin, farashin kayayyaki ya fara tashi a yankunan kudu inda kasuwannin ma babu mutane sosai.

A cewar rahoton BBC, an sayar da rago kan kudi Naira miliyan 1 a ranar Talata sannan aka sayar da wani kan kudi N800,000 a kasuwar Alaba Rago da ke Legas.

Kaji da ake siyarwa N1,500 yanzu kudinsu ya kai N2,500 sakamakon yajin aikin da ya janyo karancin kajin.

Wani mai sayar da albasa, Muhammadu Aminu, ya ce albasa da ake sayar da ita N12,000 yanzu ta kai N30,000 duk kwando.

KU KARANTA: Cacar-baki kan AK-47: Hotunan gwamnonin Bauchi da Benue sun rungumi juna bayan sulhu

Tomaturin da ake sayarwa N30 yanzu ya koma N300.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa wasu dilolin kayan abinci sun fara karkatar da kayan abincinsu zuwa kasashen Jamhuriyar Nijar da Kamaru.

Tun bayan fara yajin aikin, kungiyar ta fara rufe hanyoyin da ake bi domin kai kayan abinci jihohin kudu.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel