Zan halarci mukabalar da aka shirya mana da malaman Kano, Sheikh Kabara
- Sheikh Abduljabbar Kabara ya nuna jin dadinsa a kan ranar da Ganduje yasa na mukabalarsa da malaman Kano
- A cewar malamin, ya matukar jin dadi yadda gwamnan ya bashi damar kare kansa kuma zai samu halarta
- Kabara ya tabbatar da cewa dukkan koyarwarsa da wa'azinsa yana baiwa Annabi kariya ne, akasin zargin da ake masa
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi martani a kan wasikar da gwamnatin jihar Kano ta aika masa na ranar da za a yi mukabala tsakaninsa da malaman Kano. Ya tabbatar da cewa zai halarta.
Malamin a wata wasika da ya aikewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ce zai halarci mukabalar kuma ya yi godiya ga gwamnan a kan damar da ya bashi domin kare kansa.
Idan za mu tuna gwamnatin jihar ta saka ranar Asabar, 7 ga watan Maris domin mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da sauran malaman jihar, Daily Trust ta wallafa.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Dalibai da malaman Kagara da aka sako sun isa garin Minna
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, a wata takarda a ranar Lahadi ya ce daga Sheikh Abduljabbar da malaman Kano duk an basu wasikar wacce ke bayyana ranar mukabalar.
Amma kuma Abduljabbar ya ce dukkan koyarwarsa da wa'azinsa yana yi ne don baiwa nagartar Annabi Muhammad kariya ba kamar yadda wasu mutane ke zarginsa ba.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sako 'yan makarantar Kagara, amma akwai wasu kalubale
A wani labari na daban, hukumar tsaro ta fararen kaya (DSS) ta damke Salihu Tanko-Yakasai, mai magana da yawun gwamna Kano, Abdullahi Umar ganduje bayan ya ce gwamnatin APC ta gaza.
A ranar Juma'a, Tanko-Yakasai ya bayyana damuwarsa a kan labarin kwashe yara mata na makarantar sakandaren kwana da ke Jangebe a jihar Zamfara.
Bayan sa'o'i kadan da yin tsokacin a shafinsa a Twitter, an nemi Yakasai ko kasa ko sama an rasa, The Cable ta wallafa.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng