Hotunan taron NSC da Buhari ya yi da ministoci da shugabannin tsaro a Aso Rock

Hotunan taron NSC da Buhari ya yi da ministoci da shugabannin tsaro a Aso Rock

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi taron kwamitin tsaro na kasa da sabbin shugabannin tsaro a fadarsa ta Aso Rock da ke Abuja

- Baya ga shugabannin tsaron, wasu daga cikin ministoci da manyan ma'aikatan fadar shugaban kasa sun hallarci taron

- Taron na Kwamitin Tsaro na Kasa taro ne da ake yi duk bayan watanni hudu inda shugaban kasa ke jagoranta

Shugaba Muhammadu Buhari yana jagorantar taron Kwamaitin Tsaro na Kasa a dakin taro na Aso Rock da ke fadar shugaban kasa a Abuja, The Nation ta ruwaito.

Wannan shine taron tsaro na farko da Buhari zai yi da sabbin shugaban sojoji bayan nadinsa a karshen watan Janairu sannan majalisar tarayya ta tantance su a cikin watan Fabrairu.

DUBA WANNAN: Yadda za ka yi rajista ta yanar gizo domin zuwa yin allurar rigakafin korona cikin sauƙi

Da duminsa: Buhari, ministoci da shugabannin tsaro suna taron NSC
Da duminsa: Buhari, ministoci da shugabannin tsaro suna taron NSC. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Cikin wadanda suka hallarci taron kawai mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Shugaban Ma'aikatan Fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da NSA Manja Janar Babagaa Monguno (mai murabus).

Saura sun hada da Ministan tsaro, Janar Bashir Salihi Magashi (mai murabus), Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, Ministan harkokin yan sanda, Muhammad Dingyadi da Ministan Harkokin kasashen waje, Mr Geoffrey Onyema.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram suna taruwa a jiha ta, in ji Gwamnan Nasarawa

Shugabannin sojoji da suka hallarci taron sun hada da, Manjo Janar Lucky Irabor; Babban hafsan sojojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru; Babban hafsan sojojin sama, Air Vice Marshal Isiaka Oladayo Amoo; da babban hafsan sojojin ruwa, Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo.

Saura sun hada da sufeta janar na yan sanda Mohammed Adamu, Shugaban DSS, Yusuf Magaji Bichi, shugaban NIA, Ahmed Rufai Abubakar da shugaban DIA Manjo Janar Samuel Adebayo.

Taron na Kwamitin Tsaro na Kasa taro ne da ake yi duk bayan watanni hudu inda shugaban kasa ke jagoranta.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel