NNPC ta yi magana a kan karin kudin fetur, ta ce farashi ba zai tashi a Maris ba
- NNPC ta musanya rade-radin farashin fetur zai tashi kwanan nan a Najeriya
- Kamfanin ya ce babu shirin yin kari a lokacin da ake zama da ‘Yan kwadago
- A wata sanarwa, NNPC ta gargadi gidajen mai a kan kara kudi ko boye fetur
Kamfanin mai na kasa watau NNPC, ya ce babu karin farashin man fetur da za ayi a wannan watan na Maris.
NNPC ya gargadi mutane a kan sayen mai da ake ta yi a tsorace har ana boye wa, ya ce ba za a gamu da wani karin farashin lita a watan Maris, 2021 ba,
Wannan bayani akasin rahotannin da su ke yawo ne na cewa farashin lita zai tashi. Kamfanin yake cewa ba za su so su jefa ‘Yan Najeriya a wahala ba.
Sabon bayanin ya fito ne daga bakin mai magana da yawun bakin NNPC, Dr. Kennie Obateru.
KU KARANTA: A saurari sabon tsarin kudin litar fetur daga yanzu - 'Yan kasuwa
Darektan hulda da jama’a na NNPC, Kennie Obateru, ya bayyana cewa ba za ayi kari ba domin gudun wargaza tattaunawar da ake tsakar yi da ‘yan kwadago.
NNPC ya kum ja-kunnen gidajen mai a kan gigin karin kudi ko kuma su boye mai wanda hakan zai jawo a rika whaalar fetur na babu gaira, babu dalili a Najeriya.
Obateru ya ce a halin yanzu, NNPC na da tulin man fetur a ajiye wanda zai isa ‘Yan Najeriya har su yi fiye da kwanaki 40 su na amfani da shi ba tare da ya kare ba.
A karshe kamfanin NNPC ya yi kira ga hukumomi su sa ido domin ganin cewa gidajen mai ba su saba doka ba, tare da hukunta duk wadanda aka samu da laifi.
KU KARANTA: Man fetur: Gwamnatin Buhari ba ta tausayin talakawa - TUC
Wannan jawabi ya fito ne daga hedikwatar NNPC da ke Abuja a ranar 28 ga watan Fubrairu, 2021.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng