Yadda za ka yi rajista ta yanar gizo domin zuwa yin allurar rigakafin korona cikin sauƙi

Yadda za ka yi rajista ta yanar gizo domin zuwa yin allurar rigakafin korona cikin sauƙi

Mai taimakawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a bangaren sabbin kafafen watsa labarai, Bashir Ahmad ya ce ya yi rajista domin yin allurar rigakafin COVID-19 a shafin Hukumar Cigaban Lafiya Bai Daya ta Kasa, NPHCDANG.

A cewarsa abin babu wahala har ma an bashi rana da lokacin da zai tafi a yi masa rigakafin.

Yadda za ka yi rajitsa don yin allurar rigakafin COVID-19 ta yanar gizo
Yadda za ka yi rajitsa don yin allurar rigakafin COVID-19 ta yanar gizo.
Asali: Twitter

Ga dai yadda kowa zai iya yin rajistar domin yin rigakafin na korona.

Ka shiga shafin https://nphcdaict.com.ng/publicreg/ ta hanyar amfani da manhajar ka ta shiga yanar gizo

1. Ka cike cikakken sunan wato sunan farko na mahaifi da na iyali idan akwai

2. Ka cike lambar wayar ka

3. Ka cike adireshin imel, amma wannan ba dole bane

4. Ka bada amsa idan ka san ainihin rana, wata da shekarar da aka haife ka ko a'a

5. Cike jinsin ka, wato mace ko na miji

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Tawagar gwamnan Bauchi ta yi haɗari, 'yan sanda 10 sun jikkata

6. Rubutun irin katin shaida da ake da shi (misali, katin dan kasa, katin zabe, lasisin tuki ds)

7. Rubuta adireshin gidan da ka ke zaune

8. Rubuta jihar da ke zaune

9. Rubuta karamar hukumar da ka ke zaune

10. Rubuta gundamar da gidan ka ya ke

10a. Zabi wurin da ka ke so ka tafi yin rigakafin

10b. Zabi ranar da ka fi son ka tafi a yi maka rigakafin

10c. Zabi takamaimen lokacin da ka fi son a yi maka rigakafin

11. Dauka hoton fuskarka ka dora

KU KARANTA: Timothy ya yi basaja a matsayin Auwalu domin safarar hodar iblis ta N1bn ta bodar Sokoto

12. Shin kana aiki a bangaren lafiya ne, Eh ko A'a

13. Kana fama da wani ciwo, Eh ko A'a

14. Akwai wani irin abinci ko magani da jikinka baya so?

14. Daga karshe za a bukaci ka cike wasu lambobi hudu

A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel