Yanzu-yanzu: Tawagar gwamnan Bauchi ta yi haɗari, 'yan sanda 10 sun jikkata

Yanzu-yanzu: Tawagar gwamnan Bauchi ta yi haɗari, 'yan sanda 10 sun jikkata

- Tawagar mai girma gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ta yi haɗarin mota

- Hatsarin ya faru ne a lokacin da gwamnan da tawagarsa ke duba aikin titi a ƙaramar hukumar Tafawa Ɓalewa

- Jami'an yan sanda guda 10 sun samu rauni bayan motarsu ta yi ƙundunbala kuma a halin yanzu suna asibiti suna samun kulawan likitoci

A ƙalla ƴan sanda 10 dake ayarin Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ne suka jikkata sakamakon hatsarin mota da suka yi a ranar Litini, Daily Trust ta ruwaito.

Kamfanin Dilancin Labarai, NAN, ta ruwaito cewa hatsarin ya faru ne yayin da gwamnan ke duba aikin titi mai nisan kilomita 50 a ƙaramar hukumar Tafawa Balewa.

DUBA WANNAN: Timothy ya yi basaja a matsayin Auwalu domin safarar hodar iblis ta N1bn ta bodar Sokoto

Yanzu-yanzu: Gwamnan Bauchi Bala Mohammed da ayarinsa sunyi hastarin mota
Yanzu-yanzu: Gwamnan Bauchi Bala Mohammed da ayarinsa sunyi hastarin mota
Asali: Original

An gina titin ne domin ta hade ƙaramar hukumar Tafawa Balewa da Yelwa Duguri da ƙaramar hukumar Alkaleri na jihar.

Wakilin NAN wanda ya shaida hatsarin da idonsa ya ce mota kirar Toyota Hilux da ke dauke da ya sandan ta kwace daga titi misalin karfe 1.30 na rana ta yi kundunbala sau biyu sakamakon kwacewa direban da ta yi saboda kura da ya ke hana su ganin hanya da kyau.

KU KARANTA: Mutum 9 sun mutu, 41 sun jikkata sakamakon hatsarin mota a Kano

Amma ba bu wanda ya rasa ransa, dukkan yan sandan da hatsarin ya ritsa da su suna babban asibitin Bununu da ke karamar hukumar Tafawa Balewa ana basu kulawa.

A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel