Kamata yayi Gwamnati ta kama Gumi akan Taimakon Ta’addanci

Kamata yayi Gwamnati ta kama Gumi akan Taimakon Ta’addanci

- Guru Maharaji ya yi kira ga gwamnati ta damke Sheikh Ahmad Abubakar Gumi

- Maharaji ya shiga jerin wadanda ke zargin Sheikh Gumi da taimakawa yan bindiga

- Sheikh Gumi ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta yafewa yan bindiga kamar yadda akayiwa yan bindigan Neja Delta

Mu'assasin cocin One love family, Satguru Maharaj, ya roki gwamnatin tarayya akan ta kama Sheikh Ahmad Gumi akan zargin taimakon fashi da Ta’addanci.

A wani sako daya sawa hannu kuma ya fitar ranar Lahadi, Maharaj Ji, yace fitowar da Gumi yayi a wani shiri yana bayani akan sace-sacen fulani ya bayyanar da cewa shi wani ne da yake taimakawa fashi da Ta’addanci.

Yace yaji a shirin talabijin Gumi na cewa, Fulani suna sace mutane ne don su sami kudi, kuma basu da wata wayewa, yana sane da cewa hakan ba daidai bane kuma hatsari ne ga zaman lafiyar kasa.

KARANTA WANNAN: Dillalan shanu sun shiga hannun DSS saboda hana kai kaya Kudancin Najeriya

Kamata yayi Gwamnati ta kama Gumi akan Taimakon Ta’addanci
Kamata yayi Gwamnati ta kama Gumi akan Taimakon Ta’addanci
Asali: UGC

DUBA NAN: Jihar Benue ta saki shanu 210 ga makiyaya bayan karbar tarar Naira miliyan 5

Gumi ya kasance yana tattaunawa da shugaban Kungiyar fulani yan ta’adda, Dogo Gide da mutanensa akan sace mutane da kuma ma’aikatan Makarantar kimiyya ta kagara a jihar Niger. Wannan babban abun takaici ne," yace.

“Gumi bashi da wani dalili da zai je wajen akan tattaunawa ayi chanji na kamammu don a kubutar da rayuwar yan makaranta."

Ya kara da cewa “Muna fatan za’a dauki mataki wajen kama shi akan taimakawa fashi da ta’addanci.

“Gumi baya goyon bayan Kasa. Ayyukansa da bukatunsa sun sha banban akan ayyukan da Nigeria tasa gaba."

A wani labarin kuwa, gwamnatin jihar Kaduna ta jaddada cewa babu sasanci da zai shiga tsakaninta da 'yan bindiga duk da hauhawar miyagun ayyukansu a jihar.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya sanar da gidan talabijin na Channels a wata tattaunawa cewa 'yan bindigan da ke kawo hari duk daga jihohi masu makwabtaka ne, don haka babu dalilin sasanci da su.

Ya kara da yin bayanin cewa gwamnatin jihar tare da hadin guiwar ta tarayya suna aiki tukuru domin ganin sun shawo kan hare-haren da suka ta'azzara ballantana a kauyuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262