Mu muka garkame Salihu Tanko Yakassai, Hukumar DSS tayi amai ta lashe

Mu muka garkame Salihu Tanko Yakassai, Hukumar DSS tayi amai ta lashe

Hukumar tsaron farin kaya watau DSS ta tabbatar da cewa ita ta garkame Salihu Tanko-Yakasai tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Wannan ya biyo bayan sallamarsa da gwamnan Kanon yayi ranar Asabar.

A jawabin da kakakin hukumar DSS< Peter Afunanya ya saki da yammacin asabar, ya tabbatar da cewa lallai Tanko Yakassai na hannunsu.

Amma ya ce hukumar ta damkeshi kan wasu laifuka ne daban ba wai don ya bayyana ra'ayinsa na siyasa ba kamar yadda ake radawa a kafafen yada labarai.

"Muna tabbatar da cewa Salihu Tanko-Yakasai na hannun hukumar DSS. Ana bincikensa ne kan wasu abubuwa fiye da kalaman da ake yi a kafafen ra'ayi da sada zumunta," jawabin Peter yace.

Mu muka garkame Salihu Tanko Yakassai, Hukumar DSS tayi amai ta lashe
Mu muka garkame Salihu Tanko Yakassai, Hukumar DSS tayi amai ta lashe
Asali: UGC

Da farko, hukumar SSS, reshen jihar Kano, ta musanta kama Salihu Tanko-Yakassai, hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje saboda kalaman da ya yi na sukar Shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC mai mulki.

Idan za a iya tunawa a yayin da aka sace yaran yan makaranta a jihar Zamfara, Mr Tanko Yakasai wanda ake fi sani da Dawisu, ya shafinsa na Twitter ya bayyana cewa gwamnatin APC ta gaza.

Jim kadan bayan wallafa sakon, an rasa gano inda Yakasai ya ke a cewar abokansa don haka aka fara zargin cewa jami'an yan sandan farar hula na SSS ne suka yi awon gaba da shi.

Bayan haka Gwaman Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sallamesa kamar yadda mai taimakawa gwamnan Kano na musamman kan harkokin watsa labarai, Abubakar Aminu Ibrahim ya sanar a Twitter.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel