JAMB: Ana dab da rufe ba da gurbin karatu na zangon 2020/2021

JAMB: Ana dab da rufe ba da gurbin karatu na zangon 2020/2021

-Hukumar JAMB ta saka gindaya ranar da za ta rufe ba da gurbin karatu.

-Sannan hukumar ta ja hankalin jami'o'i kan bin ƙa'ida ta amsar ɗalibai daga wannan jami'a zuwa waccan.

-Haka kuma ta tabbatar da cewa ba za ta haɗa kai da kowa ba wajen yin abubuwan da ba su dace ba.

Jaridar Premium Times ta wallafa bayani kan cewa Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta sanar da ranar 15 ga watan Yuni a matsayin ranar ƙarshe na ba da gurbin shiga manyan makarantu.

Wannan rufewa ta shafi jarrabawar shekarar da ta gabata ne ta 2020 da aka yi domin shiga jami'o'i.

Hukumar ta fitar da wannan sanarwa ne a ranar Lahadin nan. Ga sanarwar a ƙasa:

Gurbin shiga makarantu na 2020: zuwa ga shuwagabannin manyan makarantu kan 15 ga watan Juni, 2021, ita ce ranar da za a rufe ba da gurbin karatu.

JAMB na yin kira ga bin ƙa'ida ta miƙawa da canjin kwas da makaranta kan yi...domin za a rufe dukkan dama ta ba da wani gurbin karatu a manyan makarantu na zangon karatu na shekarar 2020/2021 a 15 ga watan Juni, 2021.

Karanta wannan: Yanzu Yanzu: Jihar Katsina ta bada umarnin a sake bude makarantu

An yanke wannan shawara ne tare da dukkan shuwagabanni na manyan makarantu a wani taro da aka yi a ranar Laraba, 24 ga watan Fabarairu, 2021.

JAMB: Ana dab da rufe ba da gurbin karatu na zangon 2020/2021
JAMB: Ana dab da rufe ba da gurbin karatu na zangon 2020/2021 Tushen labari: Premium Times.
Source: UGC

A yayin da yake jawabi, rjistara na Hukumar JAMB, Prof. Is-haq Oloyede, ya bayyana cewa manufar dai taron da makarantun shi ne sanin matsayinsu dangane da ɗaukar ɗalibai na wannna shekara.

A cewarsa dai, manufar wannan taro shi ne kawo ƙarshen tsawaita tsammani na ranar ba da guraben karatu da aka yi sakamakon wannan annoba ta Kwabi-19. Ya ƙara da cewa, wannan taro zai ba su damar samar da hanyoyin da ake buƙata domin nasarar rubuta jarrabar UTME/DE.

Rijistaran ya bayyana a wurin taron cewa 30% ne na makarantu suka fara ba da guraben karatun na zangon 2020/2021.

Karanta wannan: Matsalar Tsaro: Ganduje ya sake rufe makarantun kiwon lafiya a Kano

Ya ce akwai buƙatar sanin yaushe za a rufe ɗaukar ɗaliban, sannan ya cigaba da cewa, an ba da shawara cewa, jami'o'in gwamnati su ya kamata su kammala ba da guraben da kimanin sati huɗu kafin Jami'o'i masu zaman kansu, falitakanik da kwalejojin ilimi da IEIs su yi nasu.

Bayan an gwama numfashi, mambobin sun amince da cewa duk jami'o'in gwamnati wajibi ne su kammala ba da gurbin karatu kafin 15 ga watan Mayu, 2021, inda su kuma Jami'o'i masu zaman kansu, falitakanik da kwalejojin ilimi da IEIs da COEs su ma za su yi hakan a 2021.

Mr Oloyede ya ƙara nanata wannan rana ta rufewar a matsayin hukunci na ƙarshe da kowa ya amince da shi. Sannan ya bayyana cewa hukumar za ta sanar da ranar da za a buɗe sayar da JAMB ɗin ta shekarar 2021/2022.

Haka zalika, hukumar ta buƙaci dukkan manyan makarantu da su kiyaye ƙa'idoji na canjin sheƙar daga tsangayu ko jami'o'i (intra/inter university) da kuma na ɓangaren ƙasahen waje ko kuma na canjin kwas da sauran ka'idoji na samun gurbin karatu, domin matsalar da ka iya shafar yaran da ba su jiba ba su gani ba da ka iya shafar su a lokacin tafiya Bautar ƙasa.

Ya ƙara tabbatar da cewa canja jami'i daga wannan zuwa waccan abu halastacce. Ya kuma ja hankalinsu kan cewa ƙa'idojin an tsara su ne domin yin jagoranci gare su idan aka samu irin wannan irin waɗancan mas'aloli.

Karanta wannan: Ba da ni ba: Auren jinsi ba zai taba faruwa a muulkina ba, Shugaban kasar Ghana

A karshe dai, ya ce, "JAMB ba za ta haɗa kai da kowa ba wajen yin abubuwan da ba su kamata ba ko ƙarya wata ƙa'ida. Ya kamata a bi tsararrun matakai da kuma tabbatar da in irin waɗannan ɗalibai suna da dukkan abubuwan da ake buƙata da aka gindaya domin shiga manyan makarantu."

A wani labarin kuwa, fitaccen dan gwagwarmayar nan na Yarbawa, Sunday Adeyemo, ya fara tsokano kafa Jamhuriyar Oduduwa, yana barazanar kawar da 'yan siyasar Yarbawa da zasu ki mara wa shirin nasa baya kafin 2023.

A wani faifan bidiyo da PRNigeria ta samu kuma aka fassara, Mista Igboho yayin da yake zantawa da shugabannin Yarbawa da matasa, ya ja kunnen ‘yan siyasan kan rashin nuna damuwar su ga Jamhuriyar Oduduwa.

Anas Dansalma Yakasai ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Marubuci ne mai aikin fassara da rahoto a Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.

Ku biyo ni @dansalmaanas

Source: Legit.ng

Online view pixel