Matsalar Tsaro: Ganduje ya sake rufe makarantun kiwon lafiya a Kano

Matsalar Tsaro: Ganduje ya sake rufe makarantun kiwon lafiya a Kano

-A cigaba da samun taɓarɓarewar matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.

-Gwamna ganduje na yin abin nan na hanyar lafiya a bi ta da shekara wajen rufe makarantu.

-Inda a yau ya sake rufe makarantu biyar bayan waɗanda ya rufe a baya.

The Punch ta tattaro labaran cewa, a ƙoƙarin da gwamnatin jihar Kano ke yi na kaucewa faruwar garkuwa da mutane a jihar, gwamnatin ta ba da umarnin rufe makarantu biyar da horar da jami'an kiwon lafiya cikin gaggawa.

Karanta wannan: Soyinka: Ya kamata duk jihar da ake sace yara su tsunduma zanga-zanga

Wannan umarni yana ƙunshe cikin wani bayani da mai hulɗa da jama'a na ma'aikatar lafiya ta fitar, Hadiza Mustapha Namadi ga manema labarai a ranar Lahadi.

Ganduje: Ya rufe makarantun kiwon lafiya har biyar a Kano
Ganduje: Ya rufe makarantun kiwon lafiya har biyar a Kano Tushen hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Kamar yadda yake ƙunshe cikin jawabin, sunayen makarantun da abin zai shafa sun haɗa da: School of Health Technology Bebeji, School of Nursing Madobi, da kuma Schools of Midwifery in Gwarzo da ta Gezawa and Dambatta.

Idan za mu iya tunawa, a ranar Assabar ne dai aka ba da umarnin rufe makarantun sakandire sha biyu da na manyan makarantu huɗu da ke wajen garin Kano sakamakon cigaba da taɓarɓarewar matsalar tsaro.

Karanta wannan: Arewa ba za ta iya yin nasarar jefa kuduncin ƙasar nan a yunwa ba

Kwamishinan Lafiya, Dr. Aminu Ibraim Tsanyawa, ya bayyana cewa akwai tsare-tsare na yadda ɗaliban za su cigaba da kartunsu.

Mai jawabin dai ya ba wa iyaye da masu lura da yara shawarar da su je su kwashe ƴaƴansu a safiyar wannan rana ta lahadi.

A bangare guda, Dennis Amachree, wani tsohon mataimakin darakta a hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ya ce wasu ‘yan bindiga tsoffin mambobin kungiyar Boko Haram ne, TheCable ta ruwaito.

Da yake magana lokacin da yake gabatarwa a wani shirin Arise TV a ranar Asabar, Amachree ya ce ya fahimci hakane daga ikirarin da wasu 'yan bindiga suka yi.

Ya kara da cewa ba kamar tsagerun Niger Delta da ke zanga-zangar gurbacewar yankunansu ba, 'yan bindiga ba su cancanci a yi musu afuwa ba domin su "masu laifi ne marasa alkibla"

Anas Dansalma Yakasai ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Marubuci ne mai aikin fassara da rahoto a Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.

Ku biyo ni @dansalmaanas

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng