Bayan kulle makarantun sakandare, gwamnatin Kano ta kulle wasu makarantun kwaleji 4

Bayan kulle makarantun sakandare, gwamnatin Kano ta kulle wasu makarantun kwaleji 4

- Gwamnan Kano ya sake kulle wasu makarantu don tabbatar da tsaro

- Wannan ya biyo bayan kulle wasu makarantun sakandare 10 a ranar Juma'a

Gwamnatin jihar Kano a ranar Asabar ta bada umurnin kulle wasu makarantun gaba da sakandare dake iyaka da wasu jihohin Arewa, Vanguard ta ruwaito.

Wannan ya biyo bayan garkuwa da dalibai mata 317 da aka yi a makarantar sakandaren GGSS Jangebe, karamar hukumar Talata Mafara a daren Juma'a.

Kwamishanar ilmin manyan makarantu, Dr Mariya Mahmoud Bunkure, ta ce daliban makarantun kwaleji hudu da aka bada umurnin rufewa su tattara kayansu su koma gida.

Dr Bunkure ya ce za'a sanar da dalibai lokacin da za'a sake bude makarantun.

Makarantun da za'a kulle sune:

1. Rabiu Musa Kwankwaso college of Advanced and Remedial Studies, Tudun Wada,

2. Makarantan koyar da ilmin yanayi, Gwarzo

3. Makarantar fasaha da cigaban kere-kere ( SORTED), Rano

4. ABCOAD, Dambatta.

KU KARANTA: Domin ceto daliban Jangebe, Gwamnan Zamfara ya nemi taimakon Auwalu Daudawa da dan Buharin Daji

Bayan kulle makarantun sakandare, gwamnatin Kano ta kulle wasu makarantun kwaleji 4
Bayan kulle makarantun sakandare, gwamnatin Kano ta kulle wasu makarantun kwaleji 4
Asali: Twitter

DUBA NAN: Dalibai da malaman Kagara da aka sako sun isa garin Minna

Kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta sanar da rufe makarantun kwana 10 a sassan jihar nan take biyo bayan sace yan matan makarantar GGSS Jangebe a jihar Zamfara.

Kwamishinan Ilimi na jihar, Muhammad Kiru ya ce gwamnatin ta cimma matsayin ne bayan nazari da bita kan abubuwan da ke faruwa a jihohin da ke makawabtaka da ita inda ake sace dalibai.

A cewarsa, rashin tsaron ne ya tilastawa gwamnatin daukar matakin domin kare lafiya yaran.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel