Hukumar kare hakkin yara ta ƙasa ta ba wa gwamnan Zamfara shawara

Hukumar kare hakkin yara ta ƙasa ta ba wa gwamnan Zamfara shawara

-A lokacin da ke ta cigaba da samun kiraye-kiraye kan sace yara ƴan makaranta da aka yi a Zamfara

-Wata hukuma mai kare haƙƙin yara ta ƙasa ta roƙi gwmna da sake duba matsayarsa

- Ta kuma buƙaci ƴan ta'addan da su saki yaran cikin ƙoshin lafiya

The Punch ce ta ruwaito cewa a ranar Asabar Hukumar Kare Haƙƙin Yara ta ƙasa (NHRC) ta nuna damuwarta kan yadda garkuwa da ɗalibai ke daɗi tsamari a Arewacin ƙasar nan.

Hukumar dai ta yi kira ga gwamnatin jihar Zamfara da sake duba matsayarta kan yafe wa masu garkuwa da mutane domin kaucewa iza wa wutar laifuka itace ta yadda za su riƙa sa haruɗa a zamansu da gwamnati.

KU KARANTA: An gano dajin da yan bindiga suka ajiye yan matan makarantar Jangebe

Babban ssakataren hukumar ne, Tony Ojukwu, ya bayyana haka a wani jawabi da mataimakiyar daraktan ta hulɗa da jama'a, Fatimah Mohammed, a Abuja.

A ya nuna damuwarsa a lokacin da yake ƙarɓar rahoton sace kusan ɗalibai 300 na makarantar sakandiren ƴan mata da ke Jangebe a Zamfara.

A cewarsa, ana cin mutuncin yara da maza wanda ƴan tsiraru ke yi ba tare da jin haƙi ba.

Hukumar kare hakkin yara ta ƙasa ta ba wa gwamnan Zamfara shawara
Hukumar kare hakkin yara ta ƙasa ta ba wa gwamnan Zamfara shawara Tushe: Premium Times
Asali: Twitter

Ojukwu ya ce, "Matsalar tsaro dai a Najeriya na cigaba da ƙaruwa wanda ke cigaba da ƙalubalantar jami'an tsaro, musamman na ƴan sanda, na fararen kaya, na hukumar jar kwala kan yin iya yinsu wajen ba wa mutane ƙarfin guiwar dogaro da su wajen kiyaye su."

Karanta wannan: Bayan kulle makarantun sakandare, gwamnatin Kano ta kulle wasu makarantun kwaleji 4

Sai ya cigaba, "duk da haka, muna fatan jami'an tsaro za yi ƙoƙari wajen ceto yaran nan domin ka da hakan ya shafi ɓangaren shiga makarantu na yara da kuma ce fa damar su ta samun ilimi a wani hali."

"Hukumar tana amfani da wannan dama domin kira ga gwamnatin Zamfara ta sauya ra'ayinta kan ƴan ta'addan nan ka da su riƙa zama su ne masu kafa sharuɗa a yayin kowacce irin tattaunawa."

Muna roƙon waɗannan ɓarayin mutane da su tuna yaran da ke hannunsu fa ba ruwansu kuma ba su cancanci wata cuzgunawa ba daga gare su. Don haka su sake su ba tare da wani sharaɗi ko cutarwa ba."

"NHRC na roƙon iyaye da su masu kula da yaran da wannan abu ya shafa cewa ka da su ɗauke tsammanin sake saduwa da ƴaƴansu tun da dai hukumomi a matakin jiha da ƙasa na ta ƙoƙarinsu domin kawo ƙarhsen matsalar. "

Har'ila yau, "Muna jaddada cewa hukumomi ya kamata su tabbatar da dokar haƙƙin yara ta 2003 (Child’s Rights Act 2003) kan wajibi ne yara su yi ilimi aƙalla suwa babbar sakandire. Wannan ba zai iya tabbatuwa ba a lokacin da makarantun ba sa cikin zaman lafiya."

An gargaɗi gwamnonin kasar da su daina saka wa 'yan fashi da kudi da kuma motoci domin kaucewa mummunan sakamako.

Jaridar Nigeria Tribune ta ruwaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bada wannan gargadin a ranar Juma’a, 26 ga watan Fabrairu, inda ya ce al’adar biyan wasu bata gari da wasu gwamnatocin jihohi ke yi na iya haifar da ‘da mara ido.

Anas Dansalma ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Sannan marubuci kuma mafassari da ke aiki da Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.

Ku biyo ni @dansalmaanas

Asali: Legit.ng

Online view pixel