Bidiyon wani yana rushe gidan da ya gina wa budurwarsa saboda ta ce bata son shi

Bidiyon wani yana rushe gidan da ya gina wa budurwarsa saboda ta ce bata son shi

- Wani dan kasuwa a kasar Afirka ta Kudu ya rushe wani katafaren gida da ya gina wa budurwarsa

- Dan kasuwan ya dauki wannan tsatsaurar matakin ne saboda budurwar ta ce ba za ta iya soyayya da mutum kamansa ba bayan ya gama gina mata gida

- Bisa ga dukkan alamu abinda budurwar ta yi ya fusata dan kasuwar don haka ya dako hayar motar rusau ya rusa gidan da abin da ke ciki

Masu iya magana kan yi wa soyayya kirari da ruwan zuma sai dai a wasu lokutan masoya kan yi wa juna abin mamaki idan daya daga cikinsu ya janye soyayyar ko kuma yaudara.

Wani mutum a Twitter ya bayyana yada wani dan kasuwa a kasar Afirka ta Kudu ya dauki hayar motar rusa gini domin rushe wani kyakyawan gidan da ya gina wa budurwarsa.

Bidiyon wani yana rushe gidan da ya gina wa budurwarsa saboda ta ce bata son shi
Bidiyon wani yana rushe gidan da ya gina wa budurwarsa saboda ta ce bata son shi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan auren mace mai shekaru 91 da mijinta mai shekaru 71 da aka daura bayan shekaru 10 suna soyayya

Da ya ke wallafa bidiyon a yadda ake rushe gidan, @THAB4NG ya ce matar da katse soyayyarsu ta ce bata son shi don haka dan kasuwar ya yanke shawarar ya rushe gidan da ya gina mata.

Budurwar ta jira sai da dan kasuwar ya kammala ginin gidan, ya saka mata kayan gida sannan ta fada masa bata yi har da cewa ba za ta iya soyayya da mutum kaman sa ba.

Hakan ya yi kama da cewa ta yi amfani da soyayyar ne domin amfana da arzikinsa sannan ta yi watsi da shi.

KU KARANTA: Abin da yasa muka tuba muka miƙa makamanmu, tsaffin 'yan bindigan Zamfara

Ya yi wa bidiyon lakabi da:

"Dan kasuwa ya kira motar rusa gine-gine domin rushe gidan da ya gina wa budurwarsa sakamakon rabuwa da shi da ta yi."

Ga bidiyon a kasa:

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel