Harsashin bindiga ba zai magance ƴan bindiga ba, Adamu Garba

Harsashin bindiga ba zai magance ƴan bindiga ba, Adamu Garba

- Mista Adamu Garba, tsohon dan takarar shugaban kasa ya ce harsashi ba zai yi magani yan bindiga

- Garba ya yi wannan jawabin ne yayin martani game da sace yan matan makarantar GGSS Jangebe a Zamfara

- Garba ya ce tsabar rashin adalci da manyan arewa ke yi wa talakawa ne babban dalilin kuma dole a magance hakan idan ana son zaman lafiya

Tsohon mai neman takarar shugaban kasa, Adamu Garba, a ranar Juma'a, ya ce yi wa yan bindiga ruwan harsashi ba zai kawo karshen kallubalen tsaron da ake fama da ita a kasar ba.

Garba ya yi wannan jawabin ne yayin martani a Twitter kan sace yan mata fiye da 300 daga GGSS Jangebe da ke Zamfara da wasu da ake zargin yan bindiga ne suka aikata.

Harsashin bindiga ba zai magance yan bindiga ba, Adamu Garba
Harsashin bindiga ba zai magance yan bindiga ba, Adamu Garba. Hoto: @Adamugarba
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: FAAC: Jihohi 5 da suka samu kason kudi mafi tsoka a shekarar 2020

Satar dalibai na munana a arewacin Nigeria. Mako daya da ta gabata, yan bindihan sun sace dalibai daga GSS Kagara a jihar Niger. Yan bindigan sun kuma sace dalibai 300 daga GSSS Kankara a Katsina gami da satan dalibai da aka yi a Chibok da Dapchi a jhar Borno a shekarun baya.

A wani rubutu da ya wallafa a Twitter, a ranar Juma'a, Garba ya ce idan ba a gano ainihin abinda ke sa mutane na zama yan bindigan daji an magance shi ba, za a cigaba da samun hare-haren yan bindigan a kasar.

Ya rubuta, "Muna iya tsayawa a nan mu cigaba da rubutu kan #RescueJangebeGirls amma muddin ba mu yarda cewa tsananin rashin adalci da manyan arewa ke yi wa talakawa ne ya janyo rashin tsaron ba, ko Amurka ba za ta iya magance matsalar da harsashi ba.

"Bayanai sun nuna cewa rashin kulawa ne kashe 90% na abinda ya haifar da Boko Haram. Amma kamar ba mu koyi darasi ba.

DUBA WANNAN: Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani kan sace ƴan matan makarantan Zamfara

"A maimakon mu gyara matsalar, mun gwammace su yi amfani da karfin bindiga. Gwamnati na tunanin harsashi zai magance matsalar.

"Manyan yan siyasa suna iya cigaba da rudar kansu. Amma mudin ba a magance batun rashin adalci ba, za mu cigaba da fama da wannan matsalar har sojojin mu su gaji. Ya zama dole mu magance ainihin matsalar."

A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel